Ibrahim Mohammed Kirikasama [1] (an haife shi a watan Fabrairun shekarar 1952) an zaɓe shi a matsayin Sanata mai wakiltar Jigawa ta arewa maso gabas ta jihar Jigawa, Nigeria a farkon jamhuriya ta hudu ta Najeriya, yana tsayawa takara a jam'iyyar All People's Party (APP). Ya fara aiki a ranar 29 ga Mayu 1999.[2] An sake zaɓen shi a watan Afrilun 2003 a dandalin jam'iyyar All Nigeria People's Party (ANPP) a karo na biyu na shekaru hudu.[3]

Ibrahim Muhammed Kirikasama
mamba a majalisar dattijai ta Najeriya

29 Mayu 1999 - 29 Mayu 2007 - Abdulaziz Usman
District: Jigawa North-East
Rayuwa
Haihuwa Kiri Kasama, ga Faburairu, 1952 (72 shekaru)
ƙasa Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imani
Jam'iyar siyasa All Nigeria Peoples Party
All Nigeria Peoples Party

Ayyuka da Siyasa gyara sashe

Bayan ya hau kujerarsa a Majalisar Dattawa a watan Yunin shekarata 1999 an naɗa shi kwamitocin kula da harkokin kwadago, harkokin mata, aikin gona, yaɗa labarai da ci gaban zamantakewa da wasanni.[4] Mazaɓarsa tana da muhimmanci a kogin Hadejia a fannin muhalli da tattalin arziki, wanda ke fuskantar barazanar sauye-sauyen samar da ruwa a sakamakon kogin Tiga Dam.[5][6] A wata muhawara da aka yi a watan Mayun 2006 kan ƙudirin bai wa shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo damar sake tsayawa takara karo na uku, Kirikasama ya ki amincewa da shawarar, yana mai bayyana ta a matsayin wani yunƙuri na "hallata haramtacciyar kasar da kuma tabbatar da rashin bin tsarin mulki".[7]

A zaɓen Afrilun shekarata 2007, Kirikasama ya tsaya takarar gwamnan jihar Jigawa a jam’iyyar ANPP, amma Alhaji Sule Lamido ya doke shi a jam’iyyar People’s Democratic Party da kuri’u 523,940 zuwa 260,055.[8] Jam'iyyar ANPP reshen jihar ta ki amincewa da zaɓensa a matsayin ɗan takarar.[9] Kirikasama yace ba zai ƙalubalanci nasarar Lamido ba saboda dalilai na kashin kai.[10]

Manazarta gyara sashe

  1. Kirikasama is the name of the community into which Ibrahim Mohammed was born.
  2. "FEDERAL REPUBLIC OF NIGERIA LEGISLATIVE ELECTION OF 20 FEBRUARY AND 7 MARCH 1999". Psephos. Retrieved 2010-06-21.
  3. "Senators". Dawodu. Retrieved 2010-06-21.
  4. "Congressional Committees". Nigeria Congress. Archived from the original on 18 November 2009. Retrieved 21 June 2010.
  5. Hassan H. Bdliya; Julian Barr; Steve Fraser (21 February 2006). "Institutional Failures in the Management of Critical Water Resources: The Case of the Komadugu-Yobe Basin in Nigeria" (PDF). Archived from the original (PDF) on 13 June 2011. Retrieved 21 June 2010.
  6. "Sand Dunes Overrun Northern Settlements, Advance Southwards". ThisDay. 3 August 2004. Archived from the original on 26 January 2005. Retrieved 21 June 2010.
  7. BASHIR UMAR; JAMES OJO; RAZAQ BAMIDELE (12 May 2006). "Senators knock out third term • 44 against, 39 for • 21 reps for, 18 against". Daily Sun. Archived from the original on 5 August 2007. Retrieved 21 June 2010.
  8. "How The Parties Fared". The Source Magazine. 30 April 2007. Retrieved 2010-06-21.[permanent dead link]
  9. Abdulsalam Muhammad (15 February 2007). "Caucus Rejects ANPP Guber Flag Bearer in Jigawa". Vanguard. Retrieved 2010-06-21.
  10. Michael Egbejumi-David. "Election Tribunals' Update 2: 1st August 2008". Point Blank News. Retrieved 2010-06-21.