Ibiapuye Martyns-Yellowe

Dan siyasar Najeriya (1945-2009)

Soala Ibiapuye Martyns-Yellowe an zaɓe shi a matsayin Sanata mai wakiltar Ribas ta Yamma a Jihar Ribas, Najeriya a farkon jamhuriya ta huɗu ta Najeriya, inda ta tsaya takara a ƙarƙashin jam'iyyar People's Democratic Party (PDP). Ya fara aiki a ranar 29 ga watan Mayun shekarar 1999.[1] An sake zaɓen shi a cikin watan Afrilun 2003.[2]

Ibiapuye Martyns-Yellowe
mutum
Bayanai
Bangare na Nigerian senators of the 4th National Assembly (en) Fassara
Jinsi namiji
Ƙasar asali Najeriya
Shekarun haihuwa 12 Nuwamba, 1945
Wurin haihuwa Degema
Lokacin mutuwa 2 ga Yuli, 2009
Dalilin mutuwa Fuka
Sana'a ɗan siyasa
Muƙamin da ya riƙe mamba a majalisar dattijai ta Najeriya da mamba a majalisar dattijai ta Najeriya
Ɗan bangaren siyasa Rivers State People's Democratic Party (en) Fassara da Peoples Democratic Party

An haifi Martyns-Yellowe a ranar 12 ga watan Nuwamban shekarata 1945 a Bakana, ƙaramar hukumar Degema, jihar Ribas. Ya cancanta a matsayin likitan ƙwaƙwalwa, kuma ya zama babban darektan lafiya na asibitin masu taɓin hankali na jihar Ribas, Rumuigbo, Fatakwal.[3] Bayan ya hau kujerarsa a Majalisar Dattawa a cikin watan Yunin 1999 an naɗa shi a kwamitocin kula da Magunguna da Narcotics, Man Fetur (Shugaban) da Lafiya.[4] A cikin shekarar 2007, ya kasance ɗan takara a zaɓen fidda gwani na jam’iyyar PDP don zama ɗan takarar gwamnan jihar Ribas.[3] Ya rasu ne a Abuja a ranar 2 ga watan Yulin 2009 bayan ya yi fama da cutar asma.[5]

Manazarta

gyara sashe