Hula Wata sutura ce da ake sawa a kai. A al'adar Malam Bahaushe sa hula na daga cikin cikar kamalar da namiji da suranta girma. Garuruwan da suka shahara a dunkin hula su ne kamar haka, Borno da Katsina da Paki. Hula suna ne na "tilo" jam'i kuma "Huluna". Kuma hula tana da mutukar muhimmanci a wajen mutane, musamman ma a Kasar Hausa, "cikar ado a wurin Malam Bahause sai da hula".

Wikidata.svghula
Amsterdam - Hats - 0931.jpg
Bayanai
Ƙaramin ɓangare na headgear (en) Fassara
Fabrication method (en) Fassara hatmaking (en) Fassara
Hula
Hulla

TarihiGyara

 
hular ado

Hula dai ta samo asali ne tun a ƙarnin baya, inda mutane musamman ma dattawa suka fi amfani da ita domin sanya ta a kai, hula tana kara nuna mahimmanci ga mutane a wasu ƙabilun inda wasu kuma ke sanya ta domin ado. Hula kala-kala ce kuma a Nijeriya kusan kowane yanki da yadda suke sa hula. Kuma maza su ne aka fi sani da sana'a ɗinkin hula musamman ƴan Maiduguri.[1][2]

ManazartaGyara