Hinde Bergner
Rayuwa
Haihuwa Radymno (en) Fassara, 10 Oktoba 1870
ƙasa Austria-Hungary (en) Fassara
Poland
Mutuwa Belzec extermination camp (en) Fassara, Disamba 1942
Ƴan uwa
Yara
Karatu
Harsuna Polish (en) Fassara
Sana'a
Sana'a marubuci

Hinde Bergner ( née Rosenblatt ) (ranar 10 watan Oktoba shekara ta 1870 - 1942) marubuciya ce na Yadish daga Galicia .

Tarihin Rayuwarta

gyara sashe

An haife ta a ranar 10 ga watan Oktoba, shekara ta 1870 a Radymno, Galicia (awani yanki na Daular Austro-Hungary ), daya daga cikin 'ya'ya shida na Yusufu da Bluma Rosenblatt. Mahaifinta ya mallaki rumbun ajiya na gida, kuma ana saran Hinde zata taimaka da lissafin kasuwancin iyali. Ta girma acikin dangin Hasidic, ko da yake mahaifinta yana da ɗan buɗe ido ga sabbin abubuwa na zamani, yana biyan Hinde don koyon yaren Poland, Jamusanci, da darussan duniya. Tun tana yarinya, Hinde ta gudu zuwa Jaroslaw don ta zauna da wata inna a lokacin da take tunanin iyayenta zasu hanata cigaba da karatunta. [1]

 

A shekara ta 1891, ta auri Efrayim Bergner, wanda ta haifi 'ya'ya maza uku. An haifi Moshe Bergner (daga baya Harari) a shekara ta 1892, kuma daga baya yayi hijira zuwa Falasdinu na wajibi, inda ya halarci makarantar fasaha ta Bezalel kafin ya kashe kansa yana da shekaru 21. Zakariya Bergner a shekara ta (1893-1976), ya koma Warsaw, daga baya kuma Montreal, inda ya zama fitaccen marubuci kuma mawaƙi na Yiddish a ƙarƙashin sunan alƙalami Melech Ravitch. Ɗansa Yosl Bergner acikin shekara ta(1920-2017), sanannen mai zanen Isra'ila ne. Ƙaninta, Herz Bergner cikin shekara ta(1907-1970) marubucin Yaddish marubuci ne wanda yayi hijira zuwa Ostiraliya kafin yakin duniya na biyu.

A lokacin Yaƙin Duniya na ɗaya, iyalin sunyi shekara uku a Vienna a matsayin ’yan gudun hijira. Mijinta Efrayim yayi ƙoƙari dabam-dabam sana’o’i don ya cigaba da samun kwanciyar hankali, gami da sarrafa barasa da buga rubutu, kafin mutuwarsa a shekara ta 1939. Da farkon yakin duniya na biyu, Hinde ta gudu zuwa Tarayyar Soviet, na farko zuwa Rawa Ruska ( Rava-Ruska ), Przemyśl, sa'an nan kuma zuwa Przemyślany ( Peremyshliany ), kusa da Lemberg (Lwów / Lviv). Anyi imanin cewa ta mutu a shekara ta 1942 a sansanin halakar Belzec .

Kafin mutuwarta ta aika da saƙo ga ɗanta, ta hanyar Red Cross, "Ina da rauni sosai… kwana kusa zanyi latti."

Rubutunta

gyara sashe

Hinde ta fara rubuta littafin tarihin iyali ne a cikin shekara ta 1937, wanda ta aika wa 'ya'yanta maza da yawa. Wasikunta na ƙarshe shine a cikin shekara ta 1941. Tarihinta, In di lange vinternekht, mishpokhe-zikhroynes fun a shtetl in galitsye, a shekarar 1870-1900 (A cikin dogon lokacin hunturu, abubuwan tunawa da iyali daga wani gari a Galicia, a shekara ta 1870-1900) ta bayyana kwarewar zamani da zamanantar da jama'a, da tashin hankali. hakan ya biyo baya, a yarinta shtetl . Yana da mahimmanci ga hangen nesanta na mata game da canjin al'adu da haɓakawa a cikin al'ummar Yahudawa. An buga shi bayan mutuwarsa a shekara ta cikin 1946, tare da kalmar gaba ta 'ya'yanta. Daga baya Justin Cammy ne ya fassara littafin daga Yiddish . An buga fassarar Ibrananci ta Arye Aharoni, mai suna Belelot haḥoref haarukim, zikhronot mishpaḥa meayara begalitsya, a cikin shekara ta 1982. Otto Müller ta buga fassarar Jamusanci a cikin shekara ta 1995. Fassarar Turanci, tare da gabatarwar Justin Cammy, Jami'ar Harvard Press ta buga a 2005. [2]

  1. Cite error: Invalid <ref> tag; no text was provided for refs named :0
  2. Cite error: Invalid <ref> tag; no text was provided for refs named :1