Helen Adams Keller marubuciya ce kuma mai jawabi yar kasar Amurika. An haifeta a Tuscumbia, ta jihar Alabama a 1880. Mahaifinta shine Arthur H. Keller mahaifiyarta kuma Kate Adams Keller. Tana yar watanni goma sha tara ne ta kamu da larurar da tayi sanadiyyar da ta rasa ji da ganin ta. Tana da matukar biyayya kuma gata yarinyar kirki. Magana da sauran mutane yanayi mata matukar wahala saboda bata gani kuma bata ji. Tana yin amfani da wata irin ishara ne wajen isar da sako musamman ga ahalin ta. Saidai da farko su ahalin na Helen basa fahimtar isharar tata, hakan kuma n tayar mata da hankali. Lokacin da Helen ke da shekaru bakwai be ahalin ta suka yanke shawarar nema mata malami nata na musamman. Sai suka rubuta wasika zuwa ga wani Michael Anagnos, wanda shine darakta na makarantar makafi ta Perkins Institute and Asylum for Blind. Sun rokeshi da ya taimaka masu wajen samun malamin. Sai ya dawo masu da salon cewa akwai wata matashiyar malama sunan ta Anne Sullivan. Dafarko itama makauniya ce amma bayan wata tiyata daga baya kuma sai ganinta ya dawo. Anne ta tafi zuwa Alabama inda ta zauna tare da ahalin Keller domin ta koyar da Helen a Maris 1887

Helen Keller
Rayuwa
Cikakken suna Helen Adams Keller
Haihuwa Tuscumbia (en) Fassara, 27 ga Yuni, 1880
ƙasa Tarayyar Amurka
Mazauni Coolidge Hill Road (en) Fassara
Dana Street (en) Fassara
Mutuwa Easton (en) Fassara, 1 ga Yuni, 1968
Makwanci Washington National Cathedral (en) Fassara
Yanayin mutuwa Sababi na ainihi (cuta)
Ƴan uwa
Mahaifi Arthur Henley Keller
Mahaifiya Catherine Adams
Abokiyar zama Not married
Ƴan uwa
Karatu
Makaranta Radcliffe College (en) Fassara
The Cambridge School of Weston (en) Fassara
Jami'ar Harvard
Perkins School for the Blind (en) Fassara
Matakin karatu Bachelor of Arts (en) Fassara
Harsuna Turanci
Malamai Anne Sullivan (en) Fassara
Sana'a
Sana'a marubuci, orator (en) Fassara, essayist (en) Fassara, political activist (en) Fassara, trade unionist (en) Fassara, peace activist (en) Fassara, suffragette (en) Fassara, linguist (en) Fassara da autobiographer (en) Fassara
Muhimman ayyuka The Story of My Life (en) Fassara
The Frost King (en) Fassara
Kyaututtuka
Ayyanawa daga
Mamba Industrial Workers of the World (en) Fassara
American Academy of Arts and Letters (en) Fassara
National Woman's Party (en) Fassara
Imani
Addini The New Church (en) Fassara
Jam'iyar siyasa Socialist Party of America (en) Fassara
IMDb nm0445656


Anne ta taimakama Helen wajen koya mata yadda zata runka isar da sakonni ga jama'a. Ta koya mata sunayen abubuwa ta hanyar rubuta mata sunayensu a hannun ta. Da farko Helen bata iya gane sunayen abubuwa. Kalmar farko da ta fara koya itace WATER Ruwa kenan da Hausa. Tafara da koyon kalmar ne daga lokacin da Anne ta dora hannun Helen kan ruwa inda ta rubuta mata haruffan W, A, T, E, R a hannun ta. A shekarar 1890 me ahalin Helen suka turata makarantar Perkins domin ta koyi magana. Lokacin da shekarun Helen suka kai 19 ne ta tafi kwalejin Redcliffe a Massachusetts. Ta kammala a 1904. Itace kurma-makauniya ta farko data taba samun digiri. A shekarar 1903 Helen ta rubuta littafi dangane da rayuwar ta. Sunan littafin The Story of my life ma'ana Tarihin rayuwa ta. a 1964 aka shirya wani wasan kwaikwayo maisuna The Miracle Worker dangane da rayuwar ta. Ta kuma rubuta littafi dangane da malamarta maisuna Teacher. Ta kuma rubuta wasu litattafan goma sha biyu. Helen ta tallafi masu karamin karfi da makafi lokacin rayuwarta. Tayi tafiye tafiye zuwa sama da kashe 39.

Helen Keller taso tayi aure inda ta fada soyaiya da sakataren ta, saidai mahaifiyarta bata barta ta aure shi ba saboda a lokacin masu bukata ta musamman ba'a barinsu suyi aure. Hellen Keller ta rasu a 1 ga Yuni 1968

Manazarta gyara sashe