Hawan Daba Bikin Hawan Daba sabon biki ne a ƙasar Hausa.[ana buƙatar hujja] Sabon biki a nan yana nufin ba biki ne na tun ɗauri ba, wanda Bahaushe ya gada tun kaka-da-kakanni, biki ne da ya shigo Kasar Hausa bayan zuwan Turawa.[1]

hawan daba
Hawan Daba
Hawan Daba

Tarihi gyara sashe

Ana bikin Hauwan Daba ne don sada zumunci tsakanin sarakuna ko kuma tarbar wani bako.

A wannan biki na Daba sarakuna kan haɗu da su da hakimansu kowane ɗaya da tawagarsa su hau dawakai. Za a caba musu ado.

Ana gudanar da wannan biki na Daba a filin da yake da fadi sosai. Wadancan tawagogi na sarakuna wadanda suke mahaya dawakai, za su rika zuwa suna kewayowa sannan su zo gaban Babban sarki su kawo caffa ko kuma anyi babban bakon da ake karramawa da wannan biki na Hawan Daba.

Wannan biki na Hawan Daba wata hanya ce ta kulla zumunci tsakanin sarakuna da kuma nuna wa bakon da ake karramawa dadaddiyyar al'adar da Bahaushe yake da ita.

An gudanar da Hawan Daba na farko a arewacin Najeriya a cikin shekarar 1975 a garin Kaduna domin karramawa sarauniyar Ingila.[ana buƙatar hujja]

Manazarta gyara sashe

  1. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2022-10-22. Retrieved 2022-10-22.