Hassan ll na Maroko
Hassan II (Samfuri:Langx; 9 July 1929 – 23 July 1999) ya kasance Sarkin Morroko daga 1961 har zuwa mutuwarsa a shekarar alif 1999. Memba ne na daular Alawi shine babban da ga Sarki Mohammed V,da matarsa ta biyu Gimbiya Abla bint Tahar.
An nada shi yarima a shekara ta 1957 kuma shi ne babban kwamanda na farko na Dakarun Sojojin Masarauta. An naɗa shi sarki a 1961 bayan rasuwar mahaifinsa. Sarautarsa ta zo da faruwar rikicin Yammacin Sahara da Yakin Hamada, da kuma yunkurin juyin mulki guda biyu da ba'ayi nasara a kansa ba a shekarun 1971 da 1972. Bin tafarkin ra'ayin mazan jiya na Hassan ya karfafa mulkinsa a kasar Maroko da Yammacin Sahara. An zarge shi da mulkin mallaka, da kuma tauye haƙƙin ɗan adam da cin zarafin haƙƙin 'yan ƙasa, musamman a lokacin Shekaru na Lead. An kafa kwamiti na gaskiya bayan mutuwarsa don bincika zarge-zargen keta haƙƙin ɗan adam a lokacin mulkinsa.
Rayuwa ta farko da ilimi
gyara sasheMawlay al-Hassan dan Muhammad dan Yusef al-Alawi an haife shi ne a ranar 9 ga Yulin 1929 a Dar al-Makhzen a Rabat, a lokacin mulkin mallakan Daular Faransa a Maroko, a matsayin ɗan fari ga Sultan Mohammed V da matarsa ta biyu, Lalla Abla bint Tahar, a matsayin memba na Daular Alawi [1] .[2]
Ya fara karatun kimiyyar Islama a Dar al-Makhzen a Fez. Daga nan sai ya zama dalibi a Kwalejin Masarautar a Rabat, inda ake gudanar da koyarwa a harshen Larabci da Faransanci kuma an samar masa aji. Mehdi Ben Barka ya kasance malaminsa na lissafi na tsawon shekaru hudu a Kwalejin Masarauta. [3] A watan Yunin 1948, ya sami digiri na farko daga Kwalejin Masarauatr .
Hassan ya ci gaba da karatun gaba da sakandare a Cibiyar Karatun Gaba da Sakandare ta Rabat, sashen Jami'ar Bordeaux, daga inda ya sami digiri a kan shari'a a shekarar 1951. A shekara ta 1952, ya sami digiri na biyu a fannin shari'ar jama'a daga Jami'ar Bordeaux kafin ya yi aiki a cikin Sojojin Ruwa na Faransa a cikin jirgin ruwa na Jeanne d'Arc . [4] Ya kasance dalibin digirin digirgir a Kwalejin Shari'a ta Bordeaux a 1953, lokacin da gudun hijira ta iyalinsa ta faru. Bayan ya hau gadon sarauta, a ranar 25 ga Yuni 1963, Dean Lajugie ya gabatar masa da taken Kammala Digirin Digirgir daga Jami'ar Bordeaux . [5]
Manazarta
gyara sashe- ↑ "Ahl al-Bayt". Encyclopædia Britannica (in Turanci). Archived from the original on 10 July 2022. Retrieved 10 February 2022.
- ↑ "Hassan II, king of Morocco". Encyclopædia Britannica (in Turanci). Archived from the original on 23 July 2015. Retrieved 4 February 2022.
- ↑ "قضية المهدي بن بركة تعود للواجهة بقوة في المغرب بعد مرور نصف قرن على اختطافه". CNN Arabic (in Larabci). 2015-10-30. Archived from the original on 6 March 2022. Retrieved 2022-03-06.
- ↑ "His Majesty King Hassan II". Moroccan Ministry of Communication. 2004-10-11. Archived from the original on 11 October 2004. Retrieved 2022-02-15.
- ↑ Cite error: Invalid
<ref>
tag; no text was provided for refs named:14