Harshen Punic
Punic | |
---|---|
Phoenicio-Punic, Carthaginian | |
One of the Tripolitania Punic inscriptions, in both Latin (top) and Punic (bottom) script. | |
Yanki | Tunisia, coastal parts of Algeria, Morocco, southern Iberia, Balearic islands, Libya, Malta, western Sicily, southern and eastern Sardinia |
Zamani | 8th century BC to 6th century AD |
Asali na farko | |
Phoenician alphabet | |
Lamban rijistar harshe | |
ISO 639-3 |
xpu |
xpu | |
Glottolog |
puni1241 [1]neop1239 Neo-Punic[2] |
Harshen Yaren Punic, wanda kuma ake kira Phoenicio-Punic ko Carthaginian, wani nau'i ne na Harshen Phoenician, Harshen Kan'ana na Yankin reshen Arewa maso Yammacin Semitic na yaren Harsunan Semitic. Wani reshe ne na harshen yaren Phoenician na gabar tekun Yammacin Asiya (Lebanon na zamani da arewa maso yammacin Siriya), an fi magana da shi a bakin tekun Yankin Bahar Rum na Yankin Arewa maso Yammacin Afirka, da Yankin Iberian dake da tsibirai da yawa na Bahar Rum, kamar Malta, Sicily, da Sardinia ta Mutanen Punic, ko Yammacin Phoenicians, a duk zamanin d ̄ a, daga karni na 8 BC zuwa karni na 6 AD.
Tarihi
gyara sasheTarihin Farko
gyara sasheAn yi la'akari da Punic a hankali ya rabu da iyayensa na yaren Phoenician a lokacin da Carthage ya zama babban birni na Phoenicians a ƙarƙashin Mago I, amma yunkurin masana don tsara yarukan ba su da wani daidaito tsakani kuma gabaɗaya ba su da wata yarjejeniya da rarrabuwa ba.[3]
Yan kabilar Punic sun kasance suna hulɗa da ƙasar Phoenicia har izuwa lokacin da halakar Carthage a Doron kasa ta Jamhuriyar Roma a cikin 146 BC. Da farko, babu bambanci mai wani yawa tsakanin Phoenician da Punic. Abubuwan da suka faru a cikin yaren kafin shekarar 146 BC an ɓoye su daga sauran kabilu ta hanyar bin marubutan Carthaginian ga rubutun gargajiya na kabilar Phoenician, amma akwai alamun lokaci-lokaci cewa ilimin sauti da harshe na Punic yakanyi fara bambanta da Phoenician bayan karni na shida BC.[4] Shaidar da ta fi dacewa game da wannan ta fito ne daga Motya a yammacin Sicily, amma kuma akwai alamun shi a cikin rubuce-rubucen masu wallafa na Carthaginian na ƙarni na shida kuma ba a san ko waɗannan abubuwan sun fara ne a yammacin Sicilia kuma sun bazu zuwa Yankin Afirka ko akasin haka.[4] Daga ƙarni na biyar , ana samun ka'idojin haruffa, orthographic, da phonological a rubuce-rubucen Punic a duk yammacin Bahar Rum, mai yiwuwa saboda tasirin karfin Carthaginian.[4]
Manazarta
gyara sashe- ↑ Hammarström, Harald; Forkel, Robert; Haspelmath, Martin, eds. (2017). "Punic". Glottolog 3.0. Jena, Germany: Max Planck Institute for the Science of Human History.
- ↑ Hammarström, Harald; Forkel, Robert; Haspelmath, Martin, eds. (2017). "Neo-Punic". Glottolog 3.0. Jena, Germany: Max Planck Institute for the Science of Human History.
- ↑ Empty citation (help)
- ↑ 4.0 4.1 4.2 Amadasi Guzzo 2012.