Harin Dalori, 2016
A ranar 30 ga watan Junairun shekarar 2016, aƙalla mutane 86 ne suka mutu sannan wasu aƙalla 62 suka jikkata a wani hari da mayakan Boko Haram suka kai a ƙauyen Dalori mai tazarar kilomita 4 daga birnin Maiduguri a Najeriya. Harin na ramuwar gayya ne ga rundunar haɗin gwiwa ta Civilian Task Force, kuma ya fara ne a lokacin da ƴan bindiga a cikin motoci biyu da babura suka shiga garin na Dalori suka fara harbin mutanen da ke zaune tare da tayar da bama-bamai a bukkokinsu.[1] Wani kiyasi na cewa wataƙila sama da mayakan 100 ne suka kai harin.[2] Harin ta'addancin ya kwashe tsawon kimanin sa'o'i huɗu a lokacin faruwar sa, kuma anyi zargin mayaƙan sun ƙona yara da ransu.[3]
| ||||
Iri | Kisan Kiyashi | |||
---|---|---|---|---|
Kwanan watan | 30 ga Janairu, 2016 | |||
Ƙasa | Najeriya | |||
Participant (en) | ||||
Rikici | Rikicin Boko Haram | |||
Adadin waɗanda suka rasu | 85 | |||
Adadin waɗanda suka samu raunuka | 136 |
Temako
gyara sasheSojojin Najeriya dai sun kasa fafatawa da ƴan ta’addan, sai da dakarun da aka ƙaro musu suka kai musu ɗauki, lamarin da ya sa ‘yan Boko Haram suka koma baya.[4] Ƴan ta’addan sun yi ta farautar mutanen ƙauyen da ke gudun hijira, sannan wasu mata uku ‘yan ƙuna baƙin wake sun tarwatsa kansu a cikin mutanen da suka tsere zuwa kauyen Gamori da ke makwabtaka da su.[5][6]
Alƙaluma
gyara sasheBa a dai san ainihin adadin waɗanda suka mutu ba, amma an tabbatar da mutuwar mutane akalla 86. An kuma yiwa wasu jikatattu 62 magani akan ƙunar da suka samu a asibitin kwararru na jihar dake Maiduguri. Harin yayi sanadiyyar lalata manyan sassa na ƙauyen Dalori.[4]
Alamar tambaya
gyara sasheAn dai ta ɗiga alamar tambayoyi kan yadda Mayaƙan suka kai hari a wani kauye da ke kusa da hedkwatar sojoji da ke Maiduguri, da yadda suka bi ta hanyar da sojoji da ’yan banga suka bi ba tare da tsangwama ba, da kuma yadda suka kai farmakin kauyen na sa’o’i da dama, kafin sojoji su samu nasarar dirar musu gami da iya tarwatsa su.[2]
Duba kuma
gyara sasheManazarta
gyara sashe- ↑ Reuters Editorial (31 January 2016). "At least 65 people killed in attack in Nigeria's Maiduguri". Reuters. Retrieved 31 January 2016.
- ↑ 2.0 2.1 "Another brutal attack by Boko Haram highlights the weakness of Nigeria's military". The Economist. 5 February 2016. Retrieved 8 February 2016.
- ↑ "Survivor claims Boko Haram burned kids alive in attack that kills 86". usatoday.com. USA Today. Retrieved 1 February 2016.
- ↑ 4.0 4.1 "Boko Haram blast kills scores in Nigeria's Maiduguri". Retrieved 31 January 2016.
- ↑ "Boko Haram 'burned children alive' in Nigeria village attack". Times of Malta. Press Association. 31 January 2016.
- ↑ The Guardian Newspapers. "Scores die in terrorists attack in Dalori, Borno". The Guardian Nigeria. Retrieved 31 January 2016.