Hamza Bendelladj
Rayuwa
Haihuwa Tizi Ouzou (en) Fassara, 1 ga Janairu, 1988 (36 shekaru)
ƙasa Aljeriya
Harshen uwa Arabic (en) Fassara
Karatu
Makaranta University of Science and Technology, Houari Boumediene (en) Fassara
Harsuna Larabci
Turanci
Faransanci
Sana'a
Sana'a Ma su Haking

Hanyar aiki

gyara sashe

Yayi amfani da wata software mara kyau da ake kira da suna "SpyEye", Bendelladj a ƙarƙashin sunayen "BX1" ko "Daniel HB", ya shiga na’urar kwamfutocin bankunan da masu zaman kansu don samun kalmomin shiga da lambobin Sirri tantancewa. Da zarar ya mallaki asusun, sai ya kwashe shi.

Bayan bin shekaru uku, 'yan sanda na Thai sun kama Bendelladj a ranar 7 ga watan Janairu, shekara ta 2013 yayin da yake tsayawa a Bangkok a cikin wucewa tsakanin kasar Malaysia da kasar Masar. Bai yi tsayayya da kama ba. Ya yi ban kwana da iyalinsa yayin da aka kama shi kuma matarsa da 'yarsa sun ci gaba da tafiyarsu zuwa kasar Masar ba tare da shi ba. Ya sami laƙabi "Smiling Hacker" saboda murmushi a fuskarsa yayin gabatarwar kafofin watsa labarai a duk hotunan da aka dauka bayan kama shi har ma lokacin da aka ɗaure shi. A cewar 'yan sanda na Thai, Bendelladj yana cikin manyan goma 10 da FBI ta fi nema.

Duk da bayanai da yawa na intanet Bendelladj bai sami hukuncin kisa ba, kuma yace ya ba da dukka Kuda den sadaka saboda da haka bazai yiwu a tabbatar da asusun ajiye kudaden ba Takardun shari'a ba su ambaci wani gudummawa ko ayyukan sadaka ba, suna yin jayayya da ikirarin sadaka kuma ba a san shi da tabbaci ba.[1][2]

Fitar da shi zuwa Amurka

gyara sashe

An mika shi a watan Mayu shekara ta alif dubu biyu da sha ukku 2013 zuwa kasar Amurka. An yi masa shari'a an Atlanta inda ya yi ikirarin laifi a ranar 25 ga watan Yuni, shekara ta alif dubu biyu da sha biyar 2015. Ya fuskanci hukuncin da aka yanke masa har zuwa shekaru 30 a kurkuku da kuma tarar dala miliyan goma sha huɗu.

kuma an kama abokin aikinsa Aleksandr Andreevich Panin a ranar 1 ga watan Yuli, shekara ta alif dubu biyu sha ukku 2013, a Filin jirgin saman Atlanta Hartsfield-Jackson kuma ya nemi laifi a watan Janairun 2014 shekara ta alif dubu da sha hudu a Kotun Tarayya dake kasar Atlanta.

Taimako a kan hanyoyin sadarwar jama'a

gyara sashe

An fara yada jita-jita a kan layi cewa yana fuskantar hukuncin kisa.[3] An kaddamar da takarda da ke neman Ma'aikatar Harkokin Waje ta kasar Aljeriya da Shugaba Barack Obama su shiga tsakani don a sake shi. Jakadan kasar Amurka a Aljeriya, Joan A. Polaschik ya rubuta a shafinta na Twitter cewa "laifukan na’urar kwamfuta ba laifukan hukuncin kisa ba ne kuma ba za a hukunta su da hukuncin kisa ba".

  1. "Hamza Bendelladj: Is the Algerian hacker a hero? | News". Al Jazeera. Archived from the original on 2018-01-18. Retrieved 2018-05-24.
  2. "Notorious International Computer Hackers Sentenced". Federal Bureau of Investigation (in Turanci). Archived from the original on 2020-11-12. Retrieved 2020-11-21.
  3. Hatuqa, Dalia (21 Sep 2015). "Hamza Bendelladj: Is the Algerian hacker a hero?". Al Jazeera. Retrieved 24 Apr 2024.