Halilu Obadaki(an haife shi a ranar 20 ga watan Disamba na shekara ta 1993), shi ne ɗan wasan ƙwallon ƙafa ta ƙasar Nijeriya wanda ya yi wasa a ƙungiyar Firimiya ta Nijeriya da ke Kwara United,El-Kanemi Warriors FC kuma a halin yanzu yana tare da Crown FC don Wasannin Landan Najeriyar na 2017.[1]

Halilu Obadaki
Rayuwa
Haihuwa Najeriya, 20 Disamba 1993 (31 shekaru)
Sana'a
Sana'a ɗan wasan ƙwallon ƙafa
Hanya
Ƙungiyoyi Shekaru Wasanni da ya/ta buga Ƙwallaye
  Ƙungiyar ƙwallon ƙafar ta Najeriya-
 
Muƙami ko ƙwarewa Mai buga baya
Tsayi 1.78 m

Halilu Obadaki ya fara wasansa na farko ne da Karamone inda aka gano shi kuma aka horar dashi kafin ya koma Kaduna United FC,Ranchers Bees FC da kuma Kwara United FC,inda yake taka leda tun shekara ta 2010.Ya fara buga wasan kwallon kafa na farko tare da Kaduna United FC a shekara ta 2007.Ya samu nasarar kungiyoyi biyu zuwa Firimiya Lig na Nigeria daga Pro-league Group A Winner tare da Kaduna United FC a shekara ta 2007/2008 da Nigeria National Pro-league Group A Runners-up tare da Ranchers Bees FC a shekara ta 2009/2010. Ya zira kwallaye a raga ga duk ƙungiyar ƙwallon ƙafa da ya buga koda a ƙungiyar ƙasa.[2]

== Ayyukan duniya ==

Halilu Obadaki ya kasance memba na kungiyar matasa 'yan kasa da shekaru 20 ta Najeriya da ya samu damar zuwa Gasar Afirka ta U-20 ta 2013 da kuma Kofin Duniya na U-20 na FIFA.[ana buƙatar hujja].[3]

Manazarta

gyara sashe

Hanyoyin haɗin waje

gyara sashe
  1. https://globalsportsarchive.com/people/soccer/halilu-obadaki/183006/
  2. https://www.medianigeria.com/biography-of-halilu-obadaki-footballer/[permanent dead link]
  3. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2022-03-05. Retrieved 2022-07-28.