Hajiya Zainab Maina

'yar siyasar Najeriya

Hajiya Zainab Maina, FCIA, MFR (an haife ta ranar 7 ga watan Agusta, 1948) a Jihar Adamawa da ke Arewacin Najeriya. Ta kasance tsohuwar ministan mata da walwalar jama'a ta Gwamnatin Tarayya Najeriya, wadda aka nada ta a watan Yulin shekarar 2011.[1][2]

Hajiya Zainab Maina
Minister of Women Affairs and Social Development (en) Fassara

2011 - 2015
Josephine Anenih - Aisha Alhassan
Rayuwa
Haihuwa 7 ga Augusta, 1948 (76 shekaru)
ƙasa Najeriya
Karatu
Makaranta Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Kaduna
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa

Ilimi da Rayuwa

gyara sashe

Zainab Maina ta fito ne daga jihar Adamawa dake Arewa Maso Gabashin Najeriya. Ta yi karatu a "Kaduna Polytechnic" inda ta samu Diploma a fannin Gudanarwa da kuma karatun gaba da Diploma ND a fannin girke-girke da kula a otel (Catering and Hotel Management). Bugu da kari, ta kuma samu shaidar karatun sakataranci (Secretarial Studies) a "Federal Training Centre Kaduna" , sannan kuma a cibiyar "Centre for Development & Population, Washington DC", dake USA inda ta samu karatu a kan "Institution Building Activities" .

Sannan Kuma ta auri Alhaji Umar Joji Maina, dan-Malikin Mubi dake Jihar Adamawa kuma suna da 'ya'ya tare.

Aikin Gwamnati da kuma Siyasa

gyara sashe

Kafin a ba ta matsayin minista a cikin watan Julin 2011, Maina ta kasance:

  • Board Chairman, National Commission for Nomadic Education, Kaduna (2009–2011);
  • Board Chairman, Garki Microfinance Bank (1998);
  • Board Chairman, NCWS, Garki Microfinance Bank, Abuja (1997);
  • Deputy Chairman, Police Community Relations Committee FCT Command (1998-Date);
  • Member, Vision 2010 Committee (1997);
  • Board Member, National Programme on Immunization (1998–2000);
  • Board Member, Adamawa State Primary Schools Board (1991–1994);
  • Board Member, Family Economic Advancement Programme (FEAP) (1997–2000).

Ta kasance shugabar kungiyar National Council for Women Societies (NCWS) na Najeriya. Maina na daga cikin masu fada aji a jam'iyyar PDP mai ci na lokacin sannan ta kasance memba na kwamitin dattawa na PDP, majalisar amintattu na jam'iyyar, da darekta ta musamman a fannin harkokin mata a kamfe na tshohon shugaba Jonathan da mataimakin shi Namadi Sambo (2010), Kwamitin tantance 'yan takara na jam'iyar PDP (2010); Wakiliyar mata ta kasa, Majalisar kamfe na shugaban kasa na jam'iyyar PDP (2007), Wakiliya a taron National Political Reform Conference (NPRC)-2005; Wakiliyar Mata na kwamitin sulhu na jam'iyyar PDP "PDP Reconciliation Committee on theExecutive/Legislative Impasse" (2002); Mai saukan baki na kasa da kasa na taron Home Economics and Consumer Affairs International Council of Women (ICW) da aka yi a Bangkok,Thailand (1993).[2]

Ayyukan da ba na Gwamnati ba

gyara sashe
  • Founder/President, Women for Peace Initiative (WOPI) Nigeria
  • Patron, Young Muslim Women Association, Nigeria
  • Sub-Regional Coordinator- Anglophone Africa, International Council for Women
  • Member, World Association of NGOs (WANGO)
  • Member, West African Civil Society Forum (WACSOF)
  • INGO Ambassador, International Non-Governmental Organization(London, UK)

Lambobin Yabo da Karramawa

gyara sashe
  • National Award of Excellence towards Women Development Abuja, Nigeria
  • Jean Harris Award – Rotary International
  • Winner of the Distinguished Eagle Achievement Award Newark, New Jersey, USA
  • Amazon Women Award for Contribution towards the Development of Womanhood, Lagos, Nigeria.
  • Africa Youth Congress Award on the authority of the Senate Headquarters, Banjul, the Gambia
  • Merit Award by the Mayor of Atlanta, USA
  • Meritorious Certificate for Loyal and Devoted Services to Development by the Nawar-U-Deen Society of Nigeria
  • Certificate of Recognition – University of Kansas, Lawrence, USA
  • Quintessence Award for Remarkable Contribution to Humanity by media in support of Humanity (MISH)
  • Ambassador for peace by the Universal Peace Federation and the Inter-Religious and International federation for world peace
  • Honorary citizen of Kansas City, USA
  • Fellow, African Business School – FABS
  • Fellow Chartered Institute of Administration – FCIA
  • Member of the Order of the Federal Republic – MFR

Manazarta

gyara sashe
  1. "Oduah-Ogiemwonyi is new aviation minister, Maina heads women affairs". The Sun (Nigeria). 4 July 2011. Archived from the original on 8 July 2011. Retrieved 18 July 2011.
  2. 2.0 2.1 "Hajiya Zainab Maina Biography - Age, Family". MyBioHub. 2018-06-04. Retrieved 2022-03-25.