Gidan Talabiji mai zaman kansa na Africa, wanda kuma aka fi sani da AIT, gidan talabijin ne mai zaman kansa a Najeriya. Yana aiki da Yancin Watsa Labarai a Najeriya a matsayin babbar hanyar sadarwa ta talabijin mai zaman kanta[1] mai aiki da tashoshi a cikin jihohi ashirin da hudu daga cikin talatin da shida a Najeriya. Ana kuma haska tashar AIT ta satelite daga hedkwatarta da ke Abuja.[2] AIT wani reshe ne na DAAR Communications plc, ana samunsa a duk faɗin Afirka, kuma ta kafar sadarwa na Dish har zuwa Arewacin Amurka.

Gidan Telebijin na AIT
Bayanai
Suna a hukumance
Africa Independent Television
Iri broadcast network (en) Fassara
Masana'anta broadcast network (en) Fassara
Ƙasa Najeriya
Aiki
Bangare na sherin television a najeriya
Ƙaramar kamfani na
Harshen amfani Turanci
Mulki
Hedkwata Abuja
Mamallaki Africa Independent Television
ait.live

A cikin Ƙasar Ingila da Ireland, ana iya kama tashar akan tashar Sky 454 a matsayin tasha ta kyauta (asali ana biyan kuɗi kafin samun daman kallon tasharkafin zuwa 1 Agusta 2016). Akwai wani karin tashar da ake kira AIT Movistar, wanda ke kan tashar Sky 330, ya daina watsa shirye-shirye a kan 28 Yuli 2009. AIT International ta daina watsa shirye-shirye a Burtaniya da Ireland a ranar 15 ga Oktoba 2019.

Wanda ya kafa gidan telebijin din wato Raymond Dokpesi ya jagoranci zanga-zangar lumana zuwa Majalisar Dokoki ta kasa a ranar 6 ga Yuni 2019 don gabatar da koke na neman sake duba dokokin watsa labarai.[ana buƙatar hujja]Raymond ya zanta da manema labarai da farko ya kira hankalin ‘yan jarida kan tsoma baki ta hanyar rubuce-rubuce, barazanar takunkumi da kuma son zuciya daga Darakta Janar, Modibbo Kawu[3] na Hukumar Yada Labarai ta Kasa (NBC), wanda ya kwanan nan ya fafata zaben fidda gwani a matsayin dan takarar gwamna na jam’iyyar All Progressives Congress mai mulki a jihar Kwara . Dokpesi ya kuma yi zargin cewa hukumar ta NBC na aiki ne da umarnin fadar shugaban Najeriyar na dakile ayyukan gidan talabijin din a bisa zargin karya ka’idar yada labarai.

Hukumar kula da harkokin yada labarai ta kasa ta dakatar da lasisin watsa shirye-shiryen gidan talabijin na har abada a ranar 6 ga watan Yunin 2019 bisa dalilin rashin biyan kudin lasisi da kuma amfani da labarai da ke janyo tashin hankali a shafukan sada zumunta . [4]

Sai dai wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bayar da umarnin sake bude gidan talabijin din a ranar 7 ga watan Yunin 2019. [5] [6]

  • Ohimi Amaize

Duba kuma

gyara sashe
  • Jerin gidajen talabijin a Najeriya

Manazarta

gyara sashe
  1. "Atiku, Shehu Sani, others speak on closure of AIT, Ray Power". Premium Times. Retrieved 8 December 2019.
  2. "Broadcast organisations". National Broadcasting Commission. Retrieved 23 December 2018.
  3. "Broadcast Regulator V Africa Independent Television (AIT)". Vanguard News. 9 June 2019. Retrieved 1 March 2022.
  4. NBC suspends AIT, Raypower's licenses indefinitely https://punchng.com/just-in-nbc-suspends-ait-raypowers-licences-indefinitely/amp/
  5. Court orders reopening of AIT, Raypower. https://www.premiumtimesng.com/news/headlines/333863-court-orders-reopening-of-ait-ray-power.html
  6. Court orders reopening of AIT, Raypower https://www.thecable.ng/just-in-court-orders-reopening-of-ait-raypower

Hanyoyin haɗi na waje

gyara sashe