Gibril Adamu Mohammed ɗan siyasan Ghana ne na Jamhuriyar Ghana.[1][2] Ya kasance dan majalisa mai wakiltar mazabar Asawase na yankin Ashanti na Ghana a majalisa ta 4 a jamhuriya ta hudu ta Ghana.[1][2] Ya kasance memba na National Democratic Congress.[1][2]

Gibril Adamu Mohammed
Member of the 4th Parliament of the 4th Republic of Ghana (en) Fassara

7 ga Janairu, 2005 - 15 ga Faburairu, 2005
District: Asawase Constituency (en) Fassara
Election: 2004 Ghanaian general election (en) Fassara
Rayuwa
Haihuwa 1961
ƙasa Ghana
Mutuwa 15 ga Faburairu, 2005
Karatu
Makaranta unknown value Doctor of Medicine (en) Fassara : medicine (en) Fassara
Harsuna Turanci
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa da likita
Imani
Addini Musulunci

Mohammed likita ne a sana'a.[3]

Aikin siyasa

gyara sashe

Mohammed memba a National Democratic Congress ne.[1][2] Ya zama dan majalisa ne daga watan Janairun 2005 bayan ya zama zakara a zaben gama gari a watan Disambar 2004.[1][2] An zabe shi a matsayin dan majalisa mai wakiltar mazabar Asawase a majalisa ta hudu na jamhuriyar Ghana ta hudu.[1][2]

An zabi Mohammed a matsayin dan majalisa mai wakiltar mazabar Asawase na yankin Ashanti na Ghana a karon farko a babban zaben Ghana na shekara ta 2004.[1][2] Ya yi nasara akan tikitin jam'iyyar National Democratic Congress.[1][2] Mazabarsa wani bangare ne na kujeru uku na 'yan majalisa daga cikin kujeru 39 da jam'iyyar National Democratic Congress ta samu a zaben na yankin Ashanti.[4] Jam'iyyar National Democratic Congress ta lashe kujeru 94 na 'yan majalisa daga cikin kujeru 230.[5] An zabe shi da kuri'u 33,541 daga cikin 67,485 da aka kada.[1][2] Wannan yayi daidai da 49.7% na jimlar ƙuri'un da aka jefa.[1][2] An zabe shi a kan Thomas Atigah na People's National Convention, Patricia Appiagyei na New Patriotic Party, Hassan B. A. Abu-Bong na jam'iyyar Convention People's Party, Adam Diyawu Rahaman na Democratic People's Party da Abdul Majeed Alhassan dan takara mai zaman kansa.[1][2] Wadannan sun samu kuri'u 1,598, 29,067, 570, 204 da 2,505 bi da bi na jimillar kuri'un da aka kada.[1][2] Waɗannan sun yi daidai da 2.4%, 43.1%, 0.8%, 0.3% da 3.7% na jimlar ƙuri'un da aka jefa.[1][2]

Rayuwa ta sirri

gyara sashe

Mohammed musulmi ne.[3]

Mohammed ya rasu ne jim kadan bayan ya lashe kujerar majalisar wakilai a mazabar Asawase a ranar 15 ga Fabrairun 2005.[3]

Manazarta

gyara sashe
  1. 1.00 1.01 1.02 1.03 1.04 1.05 1.06 1.07 1.08 1.09 1.10 1.11 1.12 Peace FM. "Ghana Election 2004 Results - Asawase Constituency". Ghana Elections - Peace FM. Retrieved 2020-08-02.
  2. 2.00 2.01 2.02 2.03 2.04 2.05 2.06 2.07 2.08 2.09 2.10 2.11 2.12 Elections 2004; Ghana's Parliamentary and Presidential Elections. Accra: Electoral Commission of Ghana; Friedrich Ebert Stiftung. 2005. p. 120.
  3. 3.0 3.1 3.2 Ghana Parliamentary Register, 2004-2008. Accra: The Office of Parliament. 2004.
  4. "Statistics of Presidential and Parliamentary Election Results". Fact Check Ghana (in Turanci). 2016-08-10. Retrieved 2020-08-02.
  5. Peace FM. "Ghana Election 2004 Results - President". Ghana Elections - Peace FM. Retrieved 2020-08-02.