Cif George Sodeinde Sowemimo, SAN, CON, CON, GCFR (8 ga watan Nuwambar shekarar 1920 – 29 ga watan Nuwamba shekarar 1997) wani lauyan Najeriya ne kuma tsohon Alkalin Alkalan Najeriya. Kafin zama alkalin, kotun koli, ana tunawa da Sowemimo a matsayin alkali a tuhumar da ake masa na cin amanar kasa akan zargin State v Omisade da sauransu. [1]

George Sodeinde Sowemimo
Chief Justice of Nigeria (en) Fassara

1983 - 1985
Rayuwa
Haihuwa Ogun, 8 Nuwamba, 1920
ƙasa Najeriya
Mutuwa 29 Nuwamba, 1997
Karatu
Makaranta University of Bristol (en) Fassara
Sana'a
Sana'a Lauya

Aikin alƙalanci gyara sashe

An haifi Sowemimo a Zaria a ranar 8 ga watan Nuwambar shekarar 1920, ɗan Sofoluwe da Rebecca Sowemimo. Ya halarci Makarantar Holy Trinity, Kano, sannan ya wuce CMS Grammar School, Legas . Ya yi aiki a takaice da Hukumar. Jiragen kasa ta Najeriya daga shekarar 1941 zuwa shekarar 1944. Ya samu digirin farko a fannin shari’a a Jami’ar Bristol a shekarar 1948 sannan kuma ya yi horo a Middle Temple na tsawon shekara daya kafin ya dawo kasar Najeriya ya kafa kamfaninsa na lauya. An nada shi alkalin majistare ne a shekarar 1951 sannan ya zama Babban Majistare a shekarar 1956, sannan ya kai matsayin alkali a babbar kotun Legas a shekarar 1961. A shekarar 1972 aka nada shi alkalin kotun kolin Najeriya. Bayan shafe shekaru da dama yana aiki a sashin shari'a na Najeriya, an nada shi babban jojin Najeriya a shekarar 1983 domin ya gaji marigayi Justice Atanda Fatai, Williams. Sowemimo ya yi ritaya a cikin shekarar 1985 bayan ya kai shekarun yin ritaya na doka na 65. Ya yanke hukuncin shari’ar Felony mai karfin cin amanar kasa da aka yi wa Cif Obafemi Awolowo da mukarrabansa su ashirin da shida (26).

Manazarta gyara sashe

  1. Ogundere, J. D. (1994). The Nigerian judge and his court. Ibadan. University Press. P. 97

Template:Chief Justices of Nigeria