Air Vice-Marshal George Yaw Boakye (25 ga Disamba 1937-26 ga Yuni 1979) wani sojan sama ne kuma ɗan siyasa. Tsohon kwamandan rundunar sojan saman Ghana ne (Nuwamba 1976 - Yuni 1979) kuma mamba a Supreme Military Council (SMC) a Ghana. Ya zama memba na SMC a cikin Nuwamba 1976 ta hanyar matsayinsa na Kwamandan Sojojin Sama na Ghana. An kashe shi ta hanyar harbi a ranar 26 ga Yuni 1979.

George Boakye
Rayuwa
Haihuwa 25 Disamba 1937
Mutuwa 1979
Karatu
Makaranta Opoku Ware Senior High School (en) Fassara
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa

Sake binnewa

gyara sashe
 
George Boakye

A shekara ta 2001, zawarawan Janar da Kanar da aka kashe sun roƙi Shugaba Kuffuor wanda ya ba da umarnin a tono gawarwakinsu. A ranar 27 ga watan Disambar 2001 aka mayar da kwarangwal din shugabannin sojoji na Ghana guda uku, Janar da Kanal, ga iyalansu a wani dakin ibada na sojoji; Shekaru 22 bayan kashe Janar din a daya daga cikin abubuwan da suka fi zubar da jini a kasar ta Yammacin Afirka tun bayan samun 'yancin kai. Bikin da aka yi a Accra babban birnin kasar, wanda ya samu halartar mutane sama da dubu biyu sanye da tufafin makoki na baki da ja, na daga cikin kokarin da shugaban kasar na wancan lokacin, John Kufuor ya yi, na zana layi karkashin wani babin duhu a tarihin tsohon mulkin mallaka na Birtaniya.[1] A ranar 27 ga Disamba 2001 Air Vice-Marshal Boakye da Manjo Janar Kotei, suna kwance a cikin akwatunan da aka lulluɓe da tutar ƙasar, an yi jana'izar su da cikakkiyar ɗaukakar soji a makabartar sojoji ta Osu da ke Accra.[2]

Manazarta

gyara sashe
  1. "Ghana reburies past in quest for reconciliation". General News of Friday, 28 December 2001. Ghana Home Page. Retrieved 2007-06-07.
  2. "Two Ex- military generals re-buried at Osu cemetery". General News of Friday, 28 December 2001. Ghana Home Page. Retrieved 2007-06-06.