Gbemiga Ogunleye, lauya ne dan Najeriya, ɗan jarida, masanin harkokin yaɗa labarai, kuma tsohon shugaba na Cibiyar Jarida ta Najeriya.[1][2]

Gbemiga Ogunleye
Rayuwa
Haihuwa Abeokuta, 5 ga Janairu, 1959 (65 shekaru)
ƙasa Najeriya
Harshen uwa Yarbanci
Karatu
Makaranta Jami'ar jahar Lagos
Pan-Atlantic University
Jami'ar jahar Benin
Harsuna Turanci
Yarbanci
Sana'a
Sana'a Lauya, ɗan jarida da media scholar (en) Fassara

Ya samu digirin farko a fannin shari’a daga Jami’ar Jihar Legas, sannan ya yi digiri na biyu a fannin yaɗa labarai da sadarwa daga Jami’ar Pan-Atlantic amma ya samu shaidar kammala Diploma a aikin jarida.[3] Ya kuma sami digiri na farko a fannin fasaha (BA) a fannin ilimin harsuna daga Jami'ar Benin.[4]

Ogunleye shi ne Shugaban Sadarwa na Kamfanin Arik Air, wani kamfanin jirgin sama na Najeriya da ke gudanar da zirga-zirgar jiragen sama na cikin gida, yanki da na waje.[5][6] Ya kuma kasance mataimakin babban editan jaridar The Punch, jaridar Daily Nigerian.[7] Kafin naɗa shi a matsayin shugaban Cibiyar Jarida ta Najeriya don maye gurbin Dr. Elizabeth Ikem, ya kasance darektan Labarai da al'amuran yau da kullun a TVC News, kasar Najeriya.[8]

Manazarta

gyara sashe
  1. "NIJ appoints Ogunleye, Johnson as Provost, Deputy Provost". The Eagle Online - The Nigerian Online Newspaper. Retrieved 6 April 2015.
  2. "NIGERIAN INSTITUTE OF JOURNALISM - NEWS NOW AFRICA". newsnowafrica.com. Archived from the original on 12 April 2015. Retrieved 6 April 2015.
  3. "sacks provost,elisabeth ikem Ogunleye Johnson named new provost and deputy provost". theelitesng.com. Retrieved 6 April 2015.
  4. "Ogunleye becomes NIJ provost". The Punch - Nigeria's Most Widely Read Newspaper. Archived from the original on 18 March 2015. Retrieved 6 April 2015.
  5. "EFCC Probes Arik Air Ownership Structure, Funding". proshareng.com. Retrieved 6 April 2015.
  6. "Council of Nigerian Institute of Journalism appoints new officers – Savid News, Sports, Politics". savidnews.com. Retrieved 6 April 2015.
  7. "DAME Awards". dameawards.com. Archived from the original on 25 August 2014. Retrieved 6 April 2015.
  8. "NIJ gets new provost, deputy - The Nation". The Nation. Retrieved 6 April 2015.