Gabriel Osei
Gabriel Kweku Osei dan siyasan Ghana ne kuma dan majalisar dokoki ta bakwai na jamhuriyar Ghana ta hudu mai wakiltar mazabar Tain a yankin Brong-Ahafo akan tikitin New Patriotic Party.[1][2] A halin yanzu, shi ne Jami’in Bunkasa Harkokin Kasuwanci na Babban Ofishin Ma’aikata na Kasa.[3]
Gabriel Osei | |||
---|---|---|---|
7 ga Janairu, 2017 - District: Tain Constituency (en) Election: 2016 Ghanaian general election (en) | |||
Rayuwa | |||
Haihuwa | 6 ga Faburairu, 1974 (50 shekaru) | ||
ƙasa | Ghana | ||
Karatu | |||
Makaranta |
University of Ghana Master of Philosophy (en) : Kimiyyar siyasa Kwalejin Jami'ar Katolika ta Ghana Digiri a kimiyya : business administration (en) Kwame Nkrumah University of Science and Technology Master of Business Administration (en) | ||
Harsuna | Turanci | ||
Sana'a | |||
Sana'a | ɗan siyasa da civil servant (en) | ||
Imani | |||
Addini | Kiristanci | ||
Jam'iyar siyasa | New Patriotic Party |
Rayuwar farko da ilimi
gyara sasheAn haifi Osei a ranar 2 ga Yunin shekara ta 1974 kuma ya fito ne daga Badu a yankin Brong Ahafo a lokacin, yanzu yankin Bono. Ya yi digirinsa na farko a fannin tattalin arziki a kwalejin jami'ar Katolika da ke Fiapre a shekarar 2008.[4] Sannan kuma ya samu shaidar kammala karatunsa na digiri a fannin gudanarwar kasuwanci (CEMBA) daga KNUST.[5]
Aiki
gyara sasheOsei shi ne jami’in kudi a Kwalejin Ilimi ta St. Ambrose da ke Dorma Akwamu.[4]
Siyasa
gyara sasheOsei memba ne na Sabuwar Jam'iyyar Patriotic Party. Shi ne tsohon dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Tain a yankin Bono na Ghana.[5][6][7] A babban zaben Ghana na 2020, ya sha kaye a hannun Adama Sulemana. Ya samu kuri'u 18,346 wanda ya zama kashi 40.87% na yawan kuri'un da aka kada.[8]
Tallafawa
gyara sasheA watan Oktoba 2020, ya gabatar da kusan buhunan siminti 150 don taimakawa wajen gina babbar makarantar Brodi da ofishin ‘yan sanda a mazabar.[9]
Rayuwa ta sirri
gyara sasheOsei Kirista ne.[4]
Manazarta
gyara sashe- ↑ "Parliament of Ghana". www.parliament.gh.
- ↑ "Tain MP cuts sod for 21km road construction". GhanaDistricts.com. Retrieved 2022-11-16.[permanent dead link]
- ↑ "NSS projects bumper harvest of crops". Graphic Online (in Turanci). Retrieved 2022-11-16.
- ↑ 4.0 4.1 4.2 "Osei, Gabriel". Ghana MPS (in Turanci). Retrieved 2022-11-16.
- ↑ 5.0 5.1 "Gabriel Osei, Biography". www.ghanaweb.com. Retrieved 2022-11-16.
- ↑ "Notable MPs who failed to retain their seats in the polls". Ghana News Agency (in Turanci). 2020-12-09. Retrieved 2022-11-16.
- ↑ "Infographic: NPP MPs who could not retain their seats". Happy Ghana (in Turanci). 2020-12-10. Retrieved 2022-11-16.
- ↑ FM, Peace. "Tain Constituency Results - Election 2020". Ghana Elections - Peace FM. Retrieved 2022-11-16.
- ↑ Sintim (2020-10-11). "Tain MP Hon Gabriel Osei Donates 150 bags of Cement to Brodi for Community Support". Sintim Media (in Turanci). Retrieved 2022-11-16.