Olufunke Iyabo Osibodu ko Funke Osibodu (an haife ta a shekarar 1959). ma'aikaciyar banki ce a Najeriya wadda ta jagoranci Ecobank Nigeria da Union Bank of Nigeria.

Funke Osibodu
Rayuwa
Haihuwa ga Janairu, 1959 (65 shekaru)
ƙasa Najeriya
Harshen uwa Yarbanci
Karatu
Makaranta Jami'ar Obafemi Awolowo
Makarantar Kasuwanci ta Harvard.
Harsuna Turanci
Yarbanci
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a Banker (en) Fassara da Ma'aikacin banki

Rayuwa da Karatu

gyara sashe

An haifi Funke Osibodu a cikin Janairu 1959. [1] Ta halarci Jami'ar Ife da Harvard Business School . [2]

Ta kasance shugabar kamfanin sannan daga baya ta zama darakta a kamfanin ta kuma riƙe kamfani na Ecobank Nigeria har sai da ta tafi a 2006. [3] Mijinta Victor Gbolade Osibodu ɗan kasuwar Nijeriya ne.[4]

Jagoranci

gyara sashe

Ta lura ne lokacin da aka samu tashin-tashina a harkar bankunan Najeriya lokacin da aka kori shugabannin bankunan guda biyar a ranar 13 ga Agusta 2009, kuma Babban Bankin Nijeriya ya ba da sunayen waɗanda za su maye gurbin su biyar. An zaɓe ta ne don ta jagoranci Bankin Union na Najeriya wanda ya maye gurbin Bartholomew Bassey Ebong.[5] Sauran da aka maye gurbinsu a rana guda sun haɗa da shugaban FinBank wanda aka maye gurbinsa da Suzanne Iroche.[3] An kori Ebong ne saboda bayar da rancen kudi na miliyoyin daloli ga masu hasashe waɗanda suka haɗa da Peter Ololo.

An yaba wa Osibodu saboda nuna gaskiya da ɗa'a da ta gabatar a bankin Union Bank of Nigeria. An sanya ta a matsayi ta 47 a cikin jerin manyan ƴan kasuwar mata da Jaridar Financial Times ta gabatar a shekarar 2011.[5] Ita kaɗai ce 'yar Afirka da ta shiga jerin. [6] Ta sauka daga matsayinta na shugabar bankin Union Bank a ƙarshen shekarar 2012. [7] Bayan ta bar bankin sai ta shiga harkar wutar lantarki a matsayin Shugabar Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki ta Benin zuwa Garin Benin a Najeriya [8] inda mijinta, Victor, ke Shugaban Kamfanin.

Manazarta

gyara sashe
  1. Olufunke Iyabo Osibodu, CheckCompany, Retrieved 23 February 2016
  2. New CEOs resume immediately, who they are?, Babajide Komolafe, 14 August 2009, VanguardNGR, Retrieved 23 February 2016
  3. 3.0 3.1 CBN sacks 5 Banks Directors, Gabriel Omoh and Babajide Komolafe, 14 August 2009, VanguardNGR, Retrieved 23 February 2016
  4. http://societynowng.com/Union-Bank-MD-Funke-Osibodu-Hubby-Victor-Acquire-Two-Oil-Vessels Archived 2017-02-02 at the Wayback Machine Uninon Bank MD Hubby acquires 2 Oil vessels, SocietyNowNG, Retrieved 23 February 2016
  5. 5.0 5.1 Top women, FT.com, Retrieved 24 February 2016
  6. The Other Side Of Funke Osibodu, 9 January 2016, NGRGuardianNews.com, Retrieved 24 February 2016
  7. Olufunke Iyabo Osibodu, Bloomberg, Retrieved 23 February 2016
  8. You Can Only Squeeze so Much Out of an Orange, AfricaInDC, Retrieved 23 Feb 2016