Fiona Jane Hall MBE ( née Cutts ; an haife ta a ranar 15 ga watan Yuli, shekarar 1955 a Swinton, Lancashire ) ' yar siyasar Burtaniya ce wacce ta yi memba na Majalisar Tarayyar Turai (MEP) na Arewa maso Gabashin Ingila. Ta yi aiki a matsayin shugabar jam'iyyar Liberal Democrats a majalisar Turai daga shekarar 2009 zuwa shekarar 2014. An zabe ta a Majalisar Tarayyar Turai a shekara ta 2004, sannan aka sake zabe ta a shekara ta 2009, inda ta zo ta uku a bayan 'yan takarar jam'iyyar Labour da Conservative da kashi 17% na kuri'un da aka kada, wanda shi ne mafi kolin kuri'u da dan takarar jam'iyyar Liberal Democrat na Burtaniya ya samu.

Fiona Hall ('yar siyasa)
Member of the European Parliament (en) Fassara

14 ga Yuli, 2009 - 30 ga Yuni, 2014
District: North East England (en) Fassara
Election: 2009 European Parliament election (en) Fassara
Member of the European Parliament (en) Fassara

20 ga Yuli, 2004 - 13 ga Yuli, 2009
District: North East England (en) Fassara
Election: 2004 European Parliament election (en) Fassara
Rayuwa
Haihuwa Swinton (en) Fassara, 15 ga Yuli, 1955 (69 shekaru)
ƙasa Birtaniya
Harshen uwa Turanci
Karatu
Makaranta St Hugh's College (en) Fassara
Eccles College (en) Fassara
Worsley Wardley Grammar School (en) Fassara
Harsuna Turanci
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Wurin aiki Strasbourg da City of Brussels (en) Fassara
Kyaututtuka
Imani
Jam'iyar siyasa Liberal Democrats (en) Fassara
Fiona Hall
MEP Fiona Hall, UK
Fiona Hall
Fiona Hall daga farko

Hall ta halarci Makarantar Worsley Wardley Grammar da Kwalejin Eccles. Ta ci gaba da karatu a St Hugh's College, Oxford, kuma ta kammala karatun ta na digiri a fannin Harsunan Zamani. Ta yi aiki na ɗan lokaci a matsayin malama bayan ta ƙaura zuwa Northumberland, inda ta yi yaƙi da makamashin nukiliya a farkon shekarar 1990.

Hall ta fara aiki a matsayin jami'ar siyasa na Liberal Democrats a shekara ta 1997 kuma ya kasance mai bincike na majalisa shekaru biyu bayan haka. Hall ta kasance mai kula da rumfunan zabe na Turai a Kosovo a shekara ta 2001 bayan harin bam na shekarar 1999 na NATO a Yugoslavia.

Hall ta jagoranci tawagar masu kula na Tarayyar Turai (European Union's observer) a Togo a lokacin zaben 'yan majalisar dokokin Togo a watan Oktoban, shekarar 2007 . Ta kasance mataimakiyar shugaban kungiyar Turai don Sabunta Makamashi tun daga shekarar 2008, kuma ta kasance memba a kungiyar MEPs Against Cancer .

An nada Hall a matsayin Memba na Order of the British Empire (MBE) a girmamawa na sabuwar shekara wato shekarar 2013,New Year Honours na Jerin girmamawa don ayyukan jama'a da siyasa. [1]

Manazarta

gyara sashe
  1. "No. 60367". The London Gazette (Supplement). 29 December 2012. p. 18.

Hanyoyin haɗi na waje

gyara sashe