Rabilu Musa
Rabilu Musa Ibro, anfi sanin shi da suna Ɗan Ibro (an haife shi a ranar 12 ga watan Disamba,shekarata alif 1971 – ranar 9 ga watan disamba,shekarar 2014) kwararren ɗan wasan barkwanci ne na Hausa a Najeriya, mai shiryawa, jarumi kuma mai bayar da umarni a fina-finan Hausa. Ana kallonsa a matsayin jagoran cigaban masana'antar fina finan Hausa ta Kannywood, yaciyar da masana'antar gaba sosai har zuwa rasuwar sa a shekarar 2014.[1]
Rabilu Musa | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Wudil, 12 Disamba 1971 |
ƙasa | Najeriya |
Mazauni | jahar Kano |
Harshen uwa | Hausa |
Mutuwa | jahar Kano, 9 Disamba 2014 |
Karatu | |
Harsuna | Hausa |
Sana'a | |
Sana'a | jarumi, filmmaker (en) da darakta |
Tarihin rayuwa
gyara sasheƊan Ibro ya halarci makarantar Danlasan Primary School, a garin Wudil daga baya ya je makarantar Government Teachers College Wudil duka a jahar Kano. Ya shiga aikin jami'in tsaro na gidan yari wato (Nigerian Prison Service) a 1991 yayi kuma aiyukan sakai. Daga baya kuma duka ya koma harkar fim da fim ɗin sa na farko wato yar mai Ganye wanda ya ƙara bunkasa harkokin sa.
Shahararrun wakokin da suka ƙara bunkasa shi sune bayanin Naira, Idi Wanzami, Direba Makaho
Sana'ar fim
gyara sasheRabilu Musa ya shahara sosai a harkar fina-finan hausa kaɗan daga fina-finan sa sun hada da Andamali, Bita Zai Zai, Ibro Aloko, Ibro Angon Hajiya, Ibro Dan Fulani, wasu wakoki daya shahara dasu sune Bayanin Naira, Idi Wanzami, Direba Makaho.
Fina finan
gyara sashe↓ Fim | Shekara |
---|---|
'Yar Mai Ganye | ND |
A Cuci Maza | 2013 |
Akasa Atsare | 2011 |
Allo | ND |
Andamali | 2013 |
Bita Zai Zai | ND |
Borin Ibro | ND |
Dan Auta Amalala | ND |
Dan Gatan Ibro | ND |
Dawa Dai | ND |
Gabar Ibro | ND |
Ibro Alkali | 2012 |
Ibro Aloko | 2007 |
Ibro Angon Hajiya | ND |
Ibro Ba Sulhu | 2014 |
Ibro Dan Almajiri | ND |
Ibro Dan Chacha | ND |
Ibro Dan Daudu | 2011 |
Ibro Dan Fulani | ND |
Ibro Dan Nageriya | ND |
Ibro Dan Polio | ND |
Ibro Dan Siyasa | ND |
Ibro Dan Zaki | ND |
Ibro Dawo-Dawo | 2011 |
Ibro Mahaukaci | ND |
Ibro Mai Babbar Riga | ND |
Ibro Police | ND |
Ibro Producer | 2011 |
Ibro Saye da Sayarwa | ND |
Ibro Sudan | ND |
Ibro Wuju Wuju Basu | 2011 |
Ibro Ya Auri Baturiya | 2010 |
Kankamba | ND |
Karfen Nasara | 2015 |
Kaso | ND |
Kowa Yabi | ND |
Mahauta da Fulani | ND |
Mai Dalilin Aure (Match Maker) | 2014 |
Maidaben Bagi | ND |
Mazan Baci | ND |
Namamajo | ND |
Ragon Shiri | ND |
So Kasheni | ND |
Sukuni | ND |
Tun Ran Gini | ND |
Uwar Gulma (The Mother of Gossip) | 2015 |
Kyaututtukan daya samu
gyara sasheShekara | Kyauta | Rukuni | Fim | Sakamako |
---|---|---|---|---|
2014 | 2014 Nigeria Entertainment Awards | Best Supporting Actor | Special Recognition | Nominated |
2015 | 2nd Kannywood/MTN Awards | Best Comedian (Jurors Choice Awards) | Posthumous Award | won |
Mazanarta
gyara sashe- ↑ "Dan Ibro: Exit of Kannywood^s comedy icon". Daily Trust (in Turanci). 14 December 2014. Retrieved 30 May 2022.