Fatima Hajaig
Fatima Hajaig (an haife ta a ranar 10 ga watan Disamban alif 1938) 'yar siyasar Afirka ta Kudu ce, da kuma majalisa mai mulki. Ita memba ce ta Majalisar Tarayyar Pan - Afirka daga Afirka ta Kudu . Ta kasance shugabar kwamitin harkokin kasashen waje na majalisar dokokin Afirka ta Kudu. Ta kasance Mataimakiyar Ministan Harkokin Waje a karkashin Shugaba Kgalema Motlanthe .
Fatima Hajaig | |||||
---|---|---|---|---|---|
| |||||
Rayuwa | |||||
Haihuwa | 10 Disamba 1938 (86 shekaru) | ||||
ƙasa | Afirka ta kudu | ||||
Karatu | |||||
Makaranta |
Jami'ar Witwatersrand Eötvös Loránd University (en) | ||||
Harsuna | Turanci | ||||
Sana'a | |||||
Sana'a | ɗan siyasa | ||||
Imani | |||||
Addini | Musulunci | ||||
Jam'iyar siyasa | African National Congress (en) |
Ilimi
gyara sasheHajaig ta kammala karatu daga Jami'ar Witwatersrand a 1963. A shekarar alif 1967, ta sami LLB na Jami'ar Eötvös Loránd da ke Hungary .
Tsokaci akan Yahudawa
gyara sasheA watan Disamban shekara ta 2008, ta kira sabon jakadan Isra'ila zuwa Ma'aikatar Harkokin Waje don ta soki harkokin Isra'ila a Gaza. Wannan ya haifar da korafi a hukumance daga Isra'ila ga Ofishin Jakadancin Afirka ta Kudu a Tel Aviv saboda, ya ce, Hajaig ta zagi Elias Inbram, mai magana da yawun da ya kasance haifaffen kasar Habasha na Ofishin Jakadun Isra'ila, yana zaton an kawo shi taron a matsayin baƙar fata kuma yana tambayar jakadan: [1]
Lokacin da abokan aikinka a Turai suke halartar irin wannan taro, shin suna ɗaukar wani kamar mutumin da ke zaune kusa da kai?
A wani taron COSATU a ranar Laraba 14 ga watan Janairun 2009, a Lenasia, Gauteng, ta yi sanarwa "Mulkin mallakar Amurka, kamar dau yadda yake kula da yawancin kasashen Yamma, yana karkashin kuɗaɗen Yahudawa ne kuma idan kuɗin Yahudawa ke sarrafa ƙasar ku to ba za ku iya tsammanin wani abu ba. "[2]
Ministan Harkokin Waje Nkosazana Dlamini-Zuma ya yi Allah wadai da wannan magana nata game da Yahudawa wanda ya fitar da wata sanarwa cewa irin waɗannan maganganun sun saba wa manufofin kasashen waje.[3] Kwamitin Wakilai na Yahudawa na Afirka ta Kudu ta gabatar da korafin da aka shigar a kan Hajaig ga Hukumar Kare Hakkin Dan Adam ta kasar.[2]
A ranar 3 ga watan Fabrairun shekara ta 2009 ta nemi gafara akan duk wani damuwa da ta janyo a taron. Koyaya, shugaban kwamitin wakilai na Yahudawa na Afirka ta Kudu Zev Krengel ya ce Hajaig ta ba da "gafara a fakaice" ne kawai a cikin maganarta. "Ba hakuri take bayarwa akan abunda ta ce ba. Tana bada hakuri ne akan cutarwar".
A ranar 4 ga watan Fabrairun shekara ta 2009, Shugaban Afirka ta Kudu Kgalema Motlanthe ya ba ta "horo mai tsanani" akan maganganun da ta yi game da wariyar launin fata.[4] Kwamitin Wakilan Yahudawa na Afirka ta Kudu ta yarda da neman gafara na biyu.
Tun da farko, majalisar ministoci ta "bayyana damuwa game da maganganun saboda ya saba wa manufofin da aka bayyana na wannan gwamnati game da ra'ayoyin anti-Semitic".[5]
Manazarta
gyara sashe- ↑ Belling, Michael (January 26, 2009). "Government minister's slurs anger South African Jews". Global News service of the Jewish people. Archived from the original on 2009-02-05.
- ↑ 2.0 2.1 Hirsh, David (January 29, 2009). "Minister in South African Government is anti-Jewish racist". News24. Archived from the original on 2009-01-31. Cite error: Invalid
<ref>
tag; name "bigotry" defined multiple times with different content - ↑ Anti-semitism against foreign policy: Dlamini-Zuma[dead link] The Citizen
- ↑ Staff Reporter (4 February 2009). "President raps Hajaig's knuckles". Archived from the original on 27 March 2017. Retrieved 10 May 2017.
- ↑ "Motlanthe raps Hajaig's knuckles". 4 February 2009. Archived from the original on 2009-02-10.
Samfuri:MembersSAParliament GautengSamfuri:ANC National Assembly members