Fatima Batul Mukhtar

Malama a Najeriya

Fatima Batul MukhtarAbout this soundFatima Batul Mukhtar  wata malama ce a Najeriya, wacce farfesa ce a fannin Botany. Bincike-binciken nata ya ta'allaka ne kan "tsarin bunkasuwa, kimiyyar halittu, fasahar ƙere-kere da kuma kiyaye tsirrai". A shekarar, 2016, Shugaba Muhammadu Buhari ya nada ta Mataimakiyar Shugaban Jami’ar Tarayya ta Dutse.[1]

Fatima Batul Mukhtar
Rayuwa
Haihuwa jahar Kano, 23 Mayu 1963 (61 shekaru)
ƙasa Najeriya
Karatu
Makaranta Jami'ar Bayero
Jami'ar Ahmadu Bello
Sana'a
Sana'a botanist (en) Fassara da Malami

Farkon rayuwa da Ilimi

gyara sashe

An haifi Fatima acikin garin Kano a shekara ta 1963. Ta yi makarantar firamare ta Shahuchi da kuma makarantar firamare ta ka mata ta karatun firamare, sannan ta wuce kwalejin kwana lejin 'Yan Mata ta Gwamnati, da ke Dala a garin Kano domin karatun sakandaren ta. A shekarar ta 1984, ta samu digiri a fannin ilimin tsirrai a Jami’ar Ahmadu Bello . A shekar ta 1994, ta samu digirinta na biyu a Jami’ar Bayero . Ta kammala digirinta na uku a shekara ta 2005, wacce ta ƙware a fannin ilimin kimiyyar lissafi daga wannan jami'ar. A shekara ta 2012, ta shiga kwasa-kwasan ilimin kimiyyar kere-kere a Jami'ar Jihar Michigan . Tana daya daga cikin wadanda suka assasa masu kula da harkokin ilimi a jami'ar Northwest University Kano, kuma ta sance shugabar makarantar kimiyya ta farko a jami'ar. A shekarar 2015, ta zama mataimakiyar shugabar makarantar. A shekara ta 2016, an nada ta a matsayin mataimakiyar shugaban jami'ar Tarayya ta Dutse .

Manazarta

gyara sashe
  1. "5 women who have made their marks in education". www.pulse.ng (in Turanci). 2018-03-08. Retrieved 2019-03-21.