Fasa gidan yari a Damaturu
Fasa gidan yarin Damaturu dai wani hari ne da wasu ƴan bindiga su 40, da ake kyautata zaton ƴan ƙungiyar Boko Haram ne suka kai a gidan yarin Jimeta da ke garin Damaturu babban birnin jihar Yobe a arewa maso gabashin Najeriya. Ana tunanin harin wani yunƙuri ne na ceto ƴan kungiyar Boko Haram ɗin da ke ɗaure.[1][2] Kimanin fursunoni 40 ne suka tsere daga gidan yarin; fursunoni bakwai da mai kula da gidan yari ɗaya sun mutu.[3] Fursunonin da suka tsere yawancinsu ƴan tawayen ne.[4]
Iri | aukuwa |
---|---|
Kwanan watan | 2 ga Yuni, 2012 |
Wuri | Jihar Yobe |
Adadin waɗanda suka rasu | 8 |
Lamarin
gyara sasheLamarin ya faru ne a safiyar lahadin ranar, 4 ga watan Yuni a shekara ta 2012.[5] An bayyana cewa ƴan ta’addan sun kai hari gidan yarin ne ta hanyar fadar sarkin garin, a lokacin da gwamnatin jihar Yobe ta saka dokar hana fita.[6] Shigar ƴan ta’addan a gidan yarin, ya jawo hankalin jami’an tsaron gidan yarin ɗauke da makamai da sauran jami’an tsaro da ke cikin gidan yarin, lamarin da ya sa ƴan Boko Haram ɗin suka yi musayar wuta da jami’an tsaro.[7] Waɗanda suka tseren dai ƴan ƙungiyar Boko Haram ne.[8] Fasa gidan yarin ya yi sanadiyar mutuwar fursunoni bakwai da wani jami’in gidan yarin, kuma hakan dai ya yi sanadiyyar jikkata mutane da dama.[9][10]
Duba kuma
gyara sasheManazarta
gyara sashe- ↑ "Boko Haram prison break: Radical sect frees 40 in Nigeria". Huffington Post. Archived from the original on 2014-12-29.
- ↑ "BBC News - Nigeria unrest: Inmates escape in Damaturu jail attack". BBC News.
- ↑ "Boko Haram kills eight frees 41 inmates in Damaturu prison attack". Pointblank News.
- ↑ "Boko Haram invades Damaturu Prison, frees 40 prisoners". Vanguard News.
- ↑ "Boko Haram attacks Damaturu prison, frees 40 inmates". DailyPost Nigeria.
- ↑ "Boko Haram invades Damaturu prison as explosion rocks Bauchi". Thisday. Archived from the original on 29 December 2014.
- ↑ "How gunmen raided Damaturu Prison". P.M. News Nigeria.
- ↑ "Prison break: Boko Haram attack Damaturu Prison, free 40 inmates". thenigerianvoice.com.
- ↑ "Jail break in Damaturu: 40 inmates freed". Sahara Reporters.
- ↑ "41 inmates flee as suspected Boko Haram gunmen attack Damaturu prison". The Punch - Nigeria's Most Widely Read Newspaper. Archived from the original on 29 December 2014.