Fasa gidan yari a Agodi

Yunƙurin Fasa gidan yari a Jihar Oyo

Fasa gidan yari na Agodi dai wani hari ne da aka kai a gidan yarin Agodi mafi ƙarancin tsaro da ke Ibadan babban birnin jihar Oyo a Najeriya, inda wasu masu aikata laifuka suka kai hari. An bayyana cewa; kimanin fursunoni takwas ne suka mutu a yunƙurin tserewa, da wasu goma sha takwas da suka jikkata.[1]

Infotaula d'esdevenimentFasa gidan yari a Agodi
Iri prison escape (en) Fassara
aukuwa
Kwanan watan 11 Satumba 2007
Wuri Jahar Oyo
Ƙasa Najeriya
Adadin waɗanda suka rasu 8
Adadin waɗanda suka samu raunuka 18

An ruwaito lamarin da ya faru ne a ranar 11 ga watan Satumba, 2007.[2] Wasu gungun masu laifin ne suka shirya hakan, waɗanda aka yankewa hukuncin ɗaurin rai da rai don yunƙurin tserewa daga gidan yarin.[3] Labarin ya fara ne sa’ad da mai kula da kurkukun da ke bakin aiki ya so ya baiwa fursunonin karin kumallo.[4] Nan take aka buɗe kofar suka fice daga cikin dakin da karfi da yaji, inda suka lakaɗawa jami'in duka da ƙoƙarin sakin wasu fursunoni daga cikin dakunan su.[5] Jami’an ƴan sanda sun isa wurin domin daƙile fasa gidan yarin wanda hakan ya haifar da arangama tsakanin fursunonin da ƴan sandan.[6] Hakan ya yi sanadiyar mutuwar fursunoni takwas tare da jikkata wasu goma sha takwas.[7] Yunƙurin tserewar ya ci tura, sakamakon babu wani fursuna da ya iya samun damar tserewa daga gidan yarin.[8]

Mauren Omeli, babban jami’in gidan yarin na jihar Oyo wanda ya tabbatar da harin ya yi ikirarin cewa fursunonin sun yi yunƙurin tserewa ne saboda fargabar rashin isassun kulawar lafiya.[9]

Duba kuma

gyara sashe

Manazarta

gyara sashe
  1. "Details - The Nation Archive". Retrieved 26 December 2014.
  2. "Reference at allafrica.com".
  3. Independent Newspapers Online. "Failed jail break sees eight inmates killed". Independent Online. Retrieved 26 December 2014.
  4. "Prisoners dead in Nigerian jailbreak". 12 September 2007. Retrieved 26 December 2014.
  5. "Nigerian Prisoners Die in Attempted Jailbreak". VOA. Retrieved 26 December 2014.
  6. "Nigerian Prisons And Incessant Jailbreaks - Nigerian News from Leadership Newspapers". Nigerian News from Leadership Newspapers. Archived from the original on 26 December 2014. Retrieved 26 December 2014.
  7. "Details - The Nation Archive". Retrieved 26 December 2014.
  8. "Eight shot dead in Nigeria jail break". The Sydney Morning Herald. 12 September 2007. Retrieved 26 December 2014.
  9. "BBC NEWS - Africa - Eight die in Nigeria 'jail-break'". 11 September 2007. Retrieved 26 December 2014.