Farouk El-Fishawy
Farouk El-Fishawy (Masar Larabci; 5 ga Fabrairu 1952 - 25 ga Yulin 2019) ɗan wasan fim da talabijin ne na Masar. [1] An san shi da Al-Mashbouh (1981).
Farouk El-Fishawy | |
---|---|
Rayuwa | |
Cikakken suna | محمد فاروق فهيم الفيشاوي |
Haihuwa | Sirs El-Layan (en) , 5 ga Faburairu, 1952 |
ƙasa |
Kingdom of Egypt (en) Republic of Egypt (en) United Arab Republic (en) Misra |
Harshen uwa | Larabci |
Mutuwa | Kairo, 25 ga Yuli, 2019 |
Yanayin mutuwa | Sababi na ainihi (Sankara) |
Ƴan uwa | |
Abokiyar zama |
Somaya El Alfy (en) (1974 - 1990) Soheir Ramzy (en) (1990 - 1995) |
Yara |
view
|
Karatu | |
Makaranta | Jami'ar Ain Shams |
Harsuna | Larabci |
Sana'a | |
Sana'a | jarumi, dan wasan kwaikwayon talabijin da ɗan wasan kwaikwayo |
IMDb | nm1158284 |
Rayuwa ta farko
gyara sasheAn haife shi a matsayin Mohamed Farouk El-Fishawy a Sirs El-Layan, Monufia Governorate a ranar 5 ga Fabrairun 1952. Ya kasance ɗaya daga cikin ƙannensa 3 da yayyensa 2. [2] Mahaifinsa ya rasu yana dan shekara 11 a duniya, sai babban yayansa Rashad El-Fishawy ya dauki nauyinsa ya rene shi, ya samu digirinsa na farko a fannin magunguna sannan kafin hakan ya samu digiri na farko a fannin Arts daga jami'ar Ain Shams.[3][4]
Ayyuka
gyara sasheYa fara aikinsa a cikin shekarun 1970s kuma ya fito a fina-finai da yawa da jerin talabijin. yi aiki a cikin fina-finai sama da 130, ciki har da al-Qatila (1991), al-Tufan (1985), al-Rasif (1993), Mutarada Fi al-Mamnu (1993), Ghadan Sa'antaqem (1980), Hanafy al-Obaha (1990), La Tasalni Man Ana (1984), Siriyun Lilghaya (1986), Nessa Khalf al-Qodban (1986), Qahwat al-Muaridi (1981), el-Mar'a el-Hadeya (1987), Fatat Min Israeel (1999), al-Fadiha (1992) da Dikara (1992).[5] Ya kuma yi aiki a cikin wasan kwaikwayo na talabijin.[6]
Rayuwa ta mutum
gyara sasheEl-Fishawy ya yi aure sau uku. Matarsa ta farko ita ce 'yar wasan kwaikwayo Samia al-Alfi, daga 1972 har zuwa kisan aurensu a shekarar 1992. Suna da 'ya'ya maza biyu, Omar da Ahmed . Matarsa ta biyu ita ce 'yar wasan kwaikwayo Soheir Ramzi; sun yi aure a 1992 kuma sun rabu bayan shekaru biyar, daga baya suka sake aure.[7] Matarsa ta uku ba sananniya ba ce, Nouran Mansor kuma ta rabu a shekarar 1998. [7] kuma yi dangantaka da 'yar wasan kwaikwayo Laila Elwi, amma ba su yi aure ba.[8]
Rashin lafiya da mutuwa
gyara sasheranar 3 ga Oktoba 2018, Farouk El-Fishawy, bayan ya karbi garkuwa daga Bikin Fim na Duniya na Alexandria, ya sanar da cewa yana da ciwon daji.[4]
El-Fishawy ya mutu daga ciwon daji na hanta a ranar 25 ga Yuli 2019 yana da shekaru 67.
Manazarta
gyara sashe- ↑ "Veteran actor Farouk el-Fishawy died at the age of 67". EgyptToday.
- ↑ "تعرَّف على الاسم الحقيقي للفنان فاروق الفيشاوي". www.filfan.com.
- ↑ "وفاة الفنان المصري فاروق الفيشاوي عن 67 عاما | فايزة الهنداوي". 25 July 2019.
- ↑ 4.0 4.1 "وفاة الممثل المصري فاروق الفيشاوي". 25 July 2019 – via www.bbc.com.
- ↑ "Farouq Al Fishawy - Actor Filmography، photos، Video". elCinema.com (in Turanci). Retrieved 2023-03-09.
- ↑ "السيرة الذاتية للفنان فاروق الفيشاوي وأهم أعماله الفنية". 25 July 2019.
- ↑ 7.0 7.1 "5 فنانات في حياة فاروق الفيشاوي". مجلة سيدتي. 25 July 2019.
- ↑ "شائعات وحب وصداقة.. "النص الحلو" في حياة فاروق الفيشاوي". honna.elwatannews.com.