Farooq Kperogi
Farooq Adamu Kperogi (An haifeshi ranar 30 ga watan Maris din Shekarar 1973) tshohon ɗan jarida ne kuma malamin ilimin hanyoyin sadarwa na zamani a kasar Amurka. Farooq yayi aikin jarida a gidaje jaridun Najeriya kamar Daily Trust da kuma tsohuwar jaridar New Nigerian ta gwamnatin tarayya da kuma Daily Triumph.[1]
Farooq Kperogi | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Baruten, 30 ga Maris, 1973 (51 shekaru) |
ƙasa | Najeriya |
Karatu | |
Makaranta |
Georgia State University (en) University of Louisiana at Lafayette (en) Jami'ar Bayero |
Harsuna | Turanci |
Sana'a | |
Sana'a | linguist (en) , Malami da ɗan jarida |
farooqkperogi.com |
Kperogi yana cikin masu rubuta jawabin shugaban kasa a zamanin mulkin Obasanjo, kuma ya koyar da aikin jarida a Jami'ar Ahmadu Bello da Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Kaduna. Yana koyar da aikin jarida a Jami'ar Jihar Kennesaw da ke Jojiya, Amurka.[2][3][4] Shi ne kuma marubucin (Glocal English: The Changing Face and Forms of Nigerian English), wanda aka buga a cikin shekara ta 2015, a matsayin juzu'i na 96 a cikin jerin Insights na Berkeley a cikin Linguistics da Semiotic.[5][6]
Rayuwar farkon da Ilimi
gyara sasheAn haifi Kperogi a shekara ta 1973, a Okuta, karamar hukumar Baruten a jihar Kwara, Najeriya.[7] Ya halarci Jami'ar Bayero tsakanin 1993 zuwa 1997, inda ya samu digiri na farko a fannin sadarwa. Ya sami digiri na biyu a fannin sadarwa a Jami'ar Louisiana ta Lafayette da kuma Ph.D. daga Jami'ar Jihar Jojiya a Amurka a shekara ta 2011.[2]
Bayan nan da Aiki
gyara sasheBayan kammala karatunsa a Jami'ar Bayero ta Kano, Kperogi ya fara aikin jarida a Katsina da Kano a matsayin mai kawo rahotanni, kafin ya koma Media Trust a matsayin wakilin rusasshiyar jaridar Weekly Trust. Ya kuma yi aiki da rusasshiyar jarida mallakar gwamnatin tarayya, wato jaridar New Nigerian, a farkon shekarun 2000. Kperogi ya fara aikin sa ne a tsakanin shekarar 2000 zuwa 2002 a Kwalejin kimiyya da fasaha ta Kaduna, inda ya koyar da aikin jarida da sadarwa-(journalism and mass communication). Ya kuma koyar a Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zariya na ɗan wani lokaci a shekarar 2004.[3] A tsakanin 2002 zuwa 2004, Kperogi ya yi aiki a gwamnatin Shugaba Olusegun Obasanjo a matsayin marubucin jawabin shugaban kasa kuma mai bincike. Kperogi ya rubuta ginshiƙai biyu, “Politics of Grammar" da “Notes from Atlanta”, don bugawa a jaridar Daily Trust.
Politics of Grammar
gyara sasheKperogi ya yi rubutu da yawa game da Turancin Najeriya.[8]
Notes from Atlanta
gyara sasheAikin da aka wallafa
gyara sashe- Glocal English: The Changing Face and Form of Nigerian English in Global World. New York: Peter Lang, 2015. 08033994793.ABA
Manazarta
gyara sashe- ↑ "Kperogi: The Man Who Redefined Grammar Column Writing in Nigeria". jarushub.com. JarusHub. Archived from the original on 6 October 2017. Retrieved 23 March 2018.
- ↑ 2.0 2.1 "About me". farooqkperogi.com. Farooq A. Kperogi. Retrieved 6 October 2017.
- ↑ 3.0 3.1 "Farooq Kperogi". socm.hss.kennesaw.edu. Kennesaw State University. Retrieved 6 October 2017.
- ↑ "Why British English is full of silly-sounding words". bbc.com. British Broadcasting Corporation. Retrieved 6 October 2017.
- ↑ "Berkeley Insights in Linguistics and Semiotics". www.peterlang.com. Peter Lang. Retrieved 6 October 2017.
- ↑ "7 Questions to a Linguist: Dr. Farooq Kperogi on "Glocal" English". altalang.com. ALTA. Archived from the original on 6 October 2017. Retrieved 6 October 2017.
- ↑ "Kperogi: The Man Who Redefined Grammar Column Writing in Nigeria". jarushub.com. JarusHub. Archived from the original on 6 October 2017. Retrieved 6 October 2017.
- ↑ Christine Ro (19 June 2017). "Why British English is full of silly-sounding words". BBC. Retrieved 21 January 2018.