Fadila Muhammad an haife ta a shekara ta alif 1992 -2020 Fagge Close, Unguwar Dosa, jihar Kaduna. Ta rasu a ranar 29 ga watan Agusta shekarar alif 2020. Malam Muhammad, Mahaifinta bahaushe ne kuma mahaifiyarta bafulatana ce. Fadila jarumace a masana`antar Kannywood.

Fadila Muhammad
Rayuwa
Haihuwa Unguwan Dosa (en) Fassara, 1992
ƙasa Najeriya
Mutuwa Jahar Kaduna, 29 ga Augusta, 2020
Sana'a
Sana'a jarumi

Sana'ar film

gyara sashe

Fadila wacce aka fi sani da Ummi Lollipop tafara tashe ne da ta fito a film din Kannywood mai suna "Hubbi" - fim din da yayi fice wanda ya fito da fitaccen jarumi kamar Ali Nuhu, Adam. Zango da sauransu. An yi fim din ne a shekara ta 2012, kuma ita ce shekarar da 'yar fim din da ta rasu bayan ta tsunduma cikin masana'antar Kannywood.

Fitacciyar jarumar fina-finan Kannywood, Fadila Muhammad ta bar duniya ta na yar shekara 28. Ta rasu a Kaduna a ranar Asabar 29 ga watan Agusta shekara ta 2020 sakamakon rashin lafiya a gidansu.

Manazarta

gyara sashe