Fadi Abboud ( Larabci : فادي عبود ; an haife shi ranar 21 ga Maris 1955) ɗan siyasar ƙasar Lebanon ne kuma ɗan kasuwa.

Fadi Abboud
Rayuwa
Haihuwa 21 ga Maris, 1955 (69 shekaru)
ƙasa Lebanon
Sana'a
Sana'a Mai tattala arziki, ɗan siyasa da ɗan kasuwa
Imani
Jam'iyar siyasa Free Patriotic Movement (en) Fassara

Rayuwar farko da ilimi

gyara sashe

An haifi Abboud a cikin dangin Kirista na Maronite a Sakiyat Al Misk a ranar 21 ga Maris 1955.[1][2][3] Ya yi karatu a makarantar, International School of Choueifat sannan ya karanci fannin tattalin arziki a jami'ar Westminster dake Landan.[3][4]

Abboud ya fara aikinsa a matsayin shugaban masana'antar shirya kayayyaki a shekarar 1982.[1] Sau biyu ana naɗa shi shugaban ƙungiyar masana'antun Lebanon.[5][6] Har ila yau, ya kasance memba na Cibiyar Kasuwancin Labanon ta Amirka da Cibiyar Kasuwanci ta Duniya.[5]

An naɗa shi ministan yawon buɗe ido a majalisar ministocin Saad Hariri a watan Nuwamba 2009.[1][7] An sake naɗa shi wannan muƙami a majalisar ministocin Najib Mikati a watan Yunin 2011.[8] Wa'adin Abboud ya ƙare a ranar 15 ga Fabrairu, 2014, kuma an naɗa Michel Pharoun a matsayin ministan yawon buɗe ido.[9]

Ƙungiyoyi

gyara sashe

Abboud yana da kusanci da Jam'iyyar Socialist Nationalist Party da kuma Free Patriotic Movement.[3]

Rayuwa ta sirri

gyara sashe

Abboud ya auri Sara Lilianna Saban a shekara ta 1986.[1] Suna da yara biyu.[5]

Manazarta

gyara sashe
  1. 1.0 1.1 1.2 1.3 "Resume". Official website of F. Abboud. Archived from the original on 12 January 2012. Retrieved 14 October 2012.
  2. "Biography". Katagogi. Archived from the original on 22 September 2010. Retrieved 6 March 2013.
  3. 3.0 3.1 3.2 "New Lebanese Cabinet Announced". Wikileaks. 10 November 2009. Archived from the original on 22 February 2014. Retrieved 10 March 2013.
  4. "Fady Abboud". Beirut. Retrieved 14 October 2012.
  5. 5.0 5.1 5.2 "Speakers". Astana Economic Forum. Archived from the original on 18 February 2013. Retrieved 14 October 2012.
  6. Atsuko Ichijo; Ronald Ranta (2016). Food, National Identity and Nationalism: From Everyday to Global Politics. Basingstoke; New York: Palgrave Macmillan. p. 122. ISBN 978-1-137-48313-3.
  7. "In Recognition of H.E. Minister Fady Abboud". Capitol Words. Archived from the original on 27 February 2014. Retrieved 14 October 2012.
  8. "The Cabinet". Embassy of Lebanon Washington DC. Archived from the original on 14 April 2013. Retrieved 24 October 2012.
  9. Lebanese cabinet formed after 10-month stalemate Al Arabiya. 15 February 2014. Retrieved 19 February 2014.