Ezra Olubi
Ezra Olubi ( an haife shi ne a ranar 12 ga watan Nuwamban, 1986) a Ibadan, Jihar Oyo. ɗan kasuwa ne ɗan Najeriya, ƙwararren mai fasahar watsa labarai, injiniyan na'ura me kwakwalwa kuma mai haɓaka manahajar ɗin wayar hannu. Shine CTO kuma tare da shi aka kafa babban dandalin biyan kuɗi na yanar gizo wato Paystack.[1]
Ezra Olubi | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Ibadan, 12 Nuwamba, 1986 (37 shekaru) |
ƙasa | Najeriya |
Harshen uwa | Yarbanci |
Karatu | |
Makaranta | Babcock University (en) |
Matakin karatu | computer science (en) |
Harsuna |
Turanci Yarbanci |
Sana'a | |
Sana'a | entrepreneur (en) , Furogirama da LGBTQI+ rights activist (en) |
Kyaututtuka |
gani
|
Kuruciya da Ilimi gyara sashe
An haifi Olubi a ranar 12 ga watan Nuwamba, 1986 a Ibadan. Bayan kammala karatunsa na gaba da firamari, Olubi ya tafi Jami'ar Babcock, Illishan Remo, Jihar Ogun, Najeriya, kuma ya koyi kimiyyar na'ura mai kwakwalwa tsakanin shekara ta 2002 zuwa 2006.[2]
Aiki gyara sashe
Olubi ya fara aiki ne a matsayin Manajan IT na ma'aikatat Business Management Consultants Limited, inda ya taimaka wajen haɓaka daidaita ayyukan tallace-tallace da kuma ba da kyauta manahaja. Daga baya North Ocean Logistic and Solutions Limited ta dauke shi aiki a matsayin Mai Haɓaka manahaja na Yanar Gizo.[3]