Etim Okon Inyang (25 Disamba 1931 - 26 Satumba 2016) ɗan sandan Najeriya ne kuma tsohon Sufeto Janar na ƴan sanda. An naɗa shi a cikin shekarar 1983 don ya gaji Sunday Adewusi sannan Muhammadu Gambo Jimeta ya gaje shi a cikin shekarar 1986.[1][2] Ya rasu yana da shekaru 84 a duniya a birnin Lagos dake Najeriya.

Etim Inyang
Rayuwa
Haihuwa Najeriya, 25 Disamba 1931
ƙasa Najeriya
Mutuwa 26 Satumba 2016
Karatu
Harsuna Turanci
Pidgin na Najeriya
Sana'a

Tarihi gyara sashe

An haifi Inyang a Enwang Mbo, Akwa Ibom, ɗan Okon Inyang sarkin gargajiya a Enwang. Ya yi karatunsa a Makarantar Roman Katolika, Uko-Akpan (1936 - 1937), Makarantar Methodist, Oron (1939 - 1940) da Oyubia Secondary School, Oron (1941 - 1945). Kafin ya shiga aikin ƴan sanda, Inyang malami ne a tsakanin shekarun 1946 zuwa 1949.

Aiki gyara sashe

Inyang ya shiga aikin ƴan sandan Najeriya a matsayin ɗan sanda a watan Oktoban 1949, ya zama Kofur a cikin shekarar 1957 kuma an mai da shi Kofur a cikin shekarar 1958. Ya zama Sufeto a 1958, Mataimakin Sufurtandan ƴan sanda, (1960 – 1963), Mataimakin Sufeto na ƴan sanda (1963 – 1965) da Sufeto na ƴan sanda a 1965. Ya kasance babban Sufeton ƴan sanda (1967 - 1971), Mataimakin Kwamishinan ƴan sanda (1971 - 1974), Kwamishinan ƴan sanda (1975 - 1980). Tsakanin shekarar 1961 zuwa 1971, ya kasance jami'i a ofishin INTERPOL na Sashen Bincike na Manyan Laifuka. A cikin shekarar 1974, ya gudanar da kafa hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa a rundunar ƴan sanda. Inyang ya kasance Mataimakin Sufeto Janar na ƴan sanda daga 1980 zuwa 1984 da Sufeto Janar a 1984.

Manazarta gyara sashe