Emmanuel Adjei Anhwere
Emmanuel Adjei Anhwere, (an haifeshi a ranar 20 ga watan satumba, shekarata alif dubu daya da dari tara da sittin in da biyu 1962) ɗan siyasan Ghana ne kuma ɗan majalisa a majalisar dokoki ta bakwai na jamhuriya ta huɗu ta Ghana da majalissar Ghana ta 8, mai wakiltar al'ummar mazabar Atwima-Nwabiagya ta Kudu Ashanti yankin Ghana.[1]
Emmanuel Adjei Anhwere | |||||
---|---|---|---|---|---|
7 ga Janairu, 2021 - District: Atwima Nwabiagya South Constituency (en) Election: 2020 Ghanaian general election (en)
7 ga Janairu, 2017 - 6 ga Janairu, 2021 District: Atwima Nwabiagya South Constituency (en) Election: 2016 Ghanaian general election (en) | |||||
Rayuwa | |||||
Haihuwa | Mampong (en) , 20 Satumba 1962 (62 shekaru) | ||||
ƙasa | Ghana | ||||
Karatu | |||||
Makaranta |
Kwame Nkrumah University of Science and Technology MBA (mul) : science of public administration (en) Jami'ar Ilimi, Winneba Bachelor in Business Administration (en) | ||||
Harsuna | Turanci | ||||
Sana'a | |||||
Sana'a | ɗan siyasa | ||||
Imani | |||||
Addini | Kiristanci | ||||
Jam'iyar siyasa | New Patriotic Party |
Ilimi
gyara sasheAnhwere ya sami BBA daga Jami'ar Education Winneba, a 2010. Ya wuce Jami'ar Kimiyya da Fasaha ta Kwame Nkrumah inda ya sami CEMBA (Public Administration) a 2015.[2]
Aiki da Siyasa
gyara sasheA cikin 2016, Anhwere ya tsaya a kan tikitin New Patriotic don zabar dan majalisa a majalisa ta 7 na jamhuriya ta hudu. Ya lashe zaben ne da kuri'u 48,264 cikin kuri'u 58,313 da aka kada, wanda ke wakiltar 83.15% yayin da babban abokin hamayyarsa na jam'iyyar National Democratic Party (NDC) Nana Asare Bediako, ya samu kuri'u 9,780, wanda ya wakilci kashi 16,85%. Ya ci gaba da rike kujerarsa a shekarar 2020. Babban zaben da zai wakilci mazabarsa a majalisa ta 8 a jamhuriya ta hudu. Har zuwa zabensa a shekarar 2016, ya kasance babban jami'in kula da ingancin kayayyaki na CCOBOB reshen Kumasi.[3]
Rayuwa ta sirri
gyara sasheEmmanuel magidanci ne mai ‘ya’ya biyar. Shi Kirista ne kuma yana bauta tare da cocin Anglican.[4]
Manazarta
gyara sashe- ↑ Atwima Nwabiagya, South[Ashanti-Region]. "Atwima Nwabiagya South[Ashanti-Region]". .graphic.com.gh. Graphic Communications Group. Retrieved 6 June 2017.
- ↑ "Ghana MPs - MP Details - Agyie Anhwere, Emmanuel". www.ghanamps.com. Retrieved 2021-01-10.
- ↑ "Ghana MPs - MP Details - Agyie Anhwere, Emmanuel". www.ghanamps.com. Retrieved 2021-01-10.
- ↑ "Ghana MPs - MP Details - Agyie Anhwere, Emmanuel". www.ghanamps.com. Retrieved 2021-01-10.