Ekpo Society
Ekpo (fatalwa) sigar fasahar al'adu ce wacce ta samo asali daga mutanen Efik, Ibibio da Annang a Cross River / Akwa Ibom a Kudancin Najeriya. Haka kuma yankunan da ke maƙwabtaka da su, wato Arochukwu da Ohafia ( jihar Abia ) sun ɗauki wannan al’ada a lokacin faɗaɗa masarautar Aro-Kingdom.[1][2][3]
Tarihi
gyara sasheEkpo duk ma'anar iri ɗaya ce da ta: Ekpe, Okpo-owo ko Akpo-owo kamar yadda Efik, Ibibio da Annang ke bayyana shi kawai a matsayin mutum marar rai ko mataccen rai wanda ke zuwa ƙasar masu rai.[4]
A Akwa Ibom kuwa kusan dukkan garuruwan nasu ne ake gudanar da mahalartan Ekpo musamman a lokutan bukukuwan da ake yi a Ikot Ekpene da Etim Ekpo da Oruk Anam da Abak da kuma Eket da wasu wurare a ƙasar Ibibio.[5]
A cikin ƙarni na 21
gyara sasheSaboda zuwan Kiristanci da wayewar zamani, ba a ɗaukar Ekpo a matsayin matattu waɗanda ke dawowa ƙasar masu rai; a maimakon haka, a yanzu an san shi a matsayin tufafin da mutane masu rai ke sanyawa kuma ana ɗaukar su a matsayin wani ɓangare na al'adu da gadon jama'a.[6]
Duba kuma
gyara sasheManazarta
gyara sashe- ↑ "Ekpo Ibibio" (in Turanci). Modish Project Blogs. 22 August 2016. Retrieved 2017-09-22.
- ↑ "Ekpo Annang". Naijaperminute's Blog. Archived from the original on 2017-09-23. Retrieved 2017-09-22.
- ↑ "Curses as Ekpo spirits bury dead masquerade in A'Ibom - Vanguard News". Vanguard News (in Turanci). 2018-01-23. Retrieved 2018-04-24.
- ↑ "Pictures Of Ekpo From Akwa Ibom State" (in Turanci). Wetinhappen Magazine. 26 June 2012. Retrieved 2017-09-23.
- ↑ "Ekpo Festival". Betatalk - Blogs. Archived from the original on 2017-09-24. Retrieved 2017-09-23.
- ↑ "Impact of Christianity on the Culture of AkwaIbom People". KmacIMS | Education Annex (in Turanci). 2019-05-13. Archived from the original on 2019-09-27. Retrieved 2019-09-27.