Ego (mawakiya)
Nwakaego Ihenacho Ogbaro, [1] wacce aka fi sani da Ego, mawaƙiyar Najeriya ce kuma marubuciya. Ego ta yi waƙoƙi irin su "Konko Below", "Nothing for You-(Ba komai a gare ku)" da "Never Far Away -(Kada Ku Yi Nisa)". [2] Tana yawaita zuwa yawon duniya tare da Lagbaja. Ego ta bar Africano don neman aikin solo a shekarar 2007. Daga baya ta kafa wata ƙungiya mai suna Indigo. Tun da ta bar ƙungiyar Lagbaja, ta haɗu da masu fasaha kamar Sunny Nneji, Djinee, Tosin Martins, Ayanbirin da Blaise, da sauransu. [3] Ta kuma yi wasa tare da Weird MC, Aṣa, Cobhams Asuquo da Yinka Davies . Ta fitar da wakarta mai taken "I Believe", daga kundin wakarta ta farko. Ta sanya hannun yarjejeniya a matsayin jakadiyar Globacom a 2008.[4]
Ego (mawakiya) | |
---|---|
Rayuwa | |
Cikakken suna | Nwakaego Ihenacho Ogbaro |
Haihuwa | Jahar Imo, |
ƙasa | Najeriya |
Karatu | |
Harsuna | Turanci |
Sana'a | |
Sana'a | mai rubuta waka da mawaƙi |
Sunan mahaifi | ego |
Kayan kida | murya |
Karatu
gyara sasheEgo ta yi makarantar firamare da kuma sakandaren Ikeja, GRA a Legas. Ta kammala makarantar sakandare a shekarar 1991. [5]
Duba kuma
gyara sasheManazarta
gyara sashe- ↑ "WHY I LEFT LAGBAJA –". Nollywoodgists.com. 2007-03-30. Retrieved 2020-02-05.
- ↑ "Ego". Archived from the original on 2020-11-16. Retrieved 2020-09-30.
- ↑ "Ego Ihenacho Ogbaro biography, net worth, age, family, contact & picture".
- ↑ https://www.modernghana.com/nollywood/7113/ego-and-daddy-showkey-dropped-as-globacom-amacbassadors.html Samfuri:Bare URL inline
- ↑ "Ego Ihenacho Ogbaro biography, net worth, age, family, contact & picture".