Dsamou Micheline
Dsamou Micheline (an haifi Moutio Micheline ranar 1 ga watan Yunin, shekarar 1947, a Bangaren yammacin kasar Kamaru) 'yar ƙasar Kamaru ce kuma 'yar siyasa. Ta kasance sanata a majalisar dokokin Kamaru tun a watan Maris shekarar 2018.
Dsamou Micheline | |||
---|---|---|---|
District: West (en) | |||
Rayuwa | |||
Haihuwa | Bangangté (en) , 1 ga Yuni, 1947 (77 shekaru) | ||
ƙasa | Kameru | ||
Sana'a | |||
Sana'a | ɗan siyasa |
Tarihin Rayuwa
gyara sasheYarantaka da Rayuwar Farko
gyara sasheDsamou Micheline ta halarci makarantar firamare a makarantar gwamnati a New Bell, unguwar masu aiki a cikin birnin Douala. Ta yi karatun sakandare a Kwalejin Noutong da ke Bangangté, sannan ta yi makarantar sakandare ta 'yan mata a Douala, daga karshe kuma a Lycée d'Etampes a Faransa. A farkon shekarar 1970s, ta yi rajista a Faculty of Medicine and Pharmacy a Angers, ta sami takardar shaidar kantin magani.
Sana'a
gyara sasheDsamou Micheline kuma 'yar kasuwa ce. [1] Bayan ta kammala karatunta ne ta yanke shawarar komawa ƙasar Kamaru domin bayar da gudunmuwar ci gaban ƙasar a lokacin bunƙasar tattalin arziki. [2]
Bayan dawowarta, ta sami kantin magani na Guely daga wani ɗan ƙasar Faransa. Tana da shekaru 28, ta kafa Pharmacie du Soleil a Yaoundé a cikin shekarar 1975.
A cikin shekarar 1986, ta kafa Pharmacam, kamfanin rarraba magunguna, kuma a farkon shekarun 1990, ta shiga cikin zirga-zirga da dabaru tare da ƙirƙirar Line Transit.
Ta riƙe muƙaman jagoranci a wasu kamfanoni da dama. [3]
Tafiya ta Siyasa
gyara sasheA watan Satumbar shekarar 2011, an zaɓi Dsamo Micheline a matsayin mamba a kwamitin tsakiya na jam'iyyar Dimokuraɗiyyar Jama'ar Kamaru, [4] kuma a cikin shekarar 2018, an zaɓe ta a matsayin Sanata. [5]
An sake zaɓen ta a matsayin Sanata a watan Maris 2023. [6]
Manazarta
gyara sashe- ↑ "Cameroun : La milliardaire Dsamou Micheline lance le plus gros projet agro-industriel". CamerounWeb (in Faransanci). 2023-03-07. Retrieved 2023-03-09.
- ↑ "Promotion de l'agro-industrie : un parc intégré annoncé à l'Ouest". www.cameroon-tribune.cm (in Faransanci). Retrieved 2023-03-09.
- ↑ "Cameroun : Un Parc Agro-industriel Intégré Pour Produire Plus De Huit Cents Tonnes De Riz Par An - 237online.com" (in Faransanci). 2023-03-07. Retrieved 2023-03-10.
- ↑ webmaster. "Les Membres Suppléants du comité Central". Site Web Officiel du RDPC (in Faransanci). Retrieved 2023-03-09.
- ↑ "Les Sénateurs élus du RDPC | RDPC/CPDM". senatoriales.rdpcpdm.cm. Retrieved 2023-03-09.
- ↑ admin (2023-03-24). "Cameroun-Sénatoriale 2023 : la liste des 70 sénateurs élus dévoilée". 237infos (in Faransanci). Retrieved 2023-03-24.