Dominic Ekandem
Dominic Ignatius Ekandem listen (1917 - 24 ga Nuwamba, 1995) wani Cardinal Katolika ne na Najeriya wanda ya yi aiki a matsayin Archbishop na Abuja daga shekarun 1989 zuwa 1992. Shi ne bishop na Katolika na farko ɗan asalin Afirka ta Yamma a tarihi. Ya kuma kafa kungiyar Mishan ta Saint Paul of Nigeria (MSP).
Dominic Ekandem | |||||||||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|
19 ga Yuni, 1989 -
19 ga Yuni, 1989 - 28 Satumba 1992 - John Onaiyekan → Dioceses: Roman Catholic Archdiocese of Abuja (en)
24 Mayu 1976 -
1 ga Maris, 1963 - Dioceses: Roman Catholic Diocese of Ikot Ekpene (en)
7 ga Augusta, 1953 - Dioceses: Roman Catholic Archdiocese of Calabar (en)
7 ga Augusta, 1953 - Dioceses: Hierapolis in Isauria (en) | |||||||||||||
Rayuwa | |||||||||||||
Haihuwa | Najeriya, 23 ga Yuni, 1917 | ||||||||||||
ƙasa | Najeriya | ||||||||||||
Mutuwa | Abuja, 24 Nuwamba, 1995 | ||||||||||||
Sana'a | |||||||||||||
Sana'a | Malamin akida, Catholic priest (en) da Catholic bishop (en) | ||||||||||||
Mahalarcin
| |||||||||||||
Imani | |||||||||||||
Addini | Cocin katolika |
Ɗan asalin jihar Akwa Ibom, Ekandem ya halarci makarantun ɗarikar Katolika da dama kafin ya zama limamin coci. An naɗa shi a ranar 7 ga watan Disamba 1947, kuma ya zama firist na farko daga tsohuwar lardin Calabar. Aikinsa na farko a matsayin bishop shine mataimakin Calabar daga shekarun 1953 zuwa 1963. Ya kasance Bishop na Ikot Ekpene daga shekarun 1963 zuwa 1981; a lokacin, a cikin watan Afrilu 1976, an naɗa shi a matsayin Cardinal. Sannan ya zama Babban Malami na Abuja, kuma lokacin da Abuja ta zama Archdiocese a shekarar 1989, ya zama Archbishop (Personal title).[1]
Ekandem ya rasu a shekarar 1995.