Dadis Mousa Camara
Moussa Dadis Camara (an haifeshi a shekarar 1964 a garin Koule dake kusa da Nzerekore- a ƙasar ta Guinea.
Dadis Mousa Camara | |||
---|---|---|---|
24 Disamba 2008 - 3 Disamba 2009 ← Lansana Conté (en) - Sékouba Konaté (en) → | |||
Rayuwa | |||
Haihuwa | Koure (en) , 29 Disamba 1964 (59 shekaru) | ||
ƙasa | Gine | ||
Ƴan uwa | |||
Abokiyar zama | Jeanne Saba (en) | ||
Karatu | |||
Makaranta | University of Conakry (en) | ||
Harsuna | Faransanci | ||
Sana'a | |||
Sana'a | soja da ɗan siyasa | ||
Imani | |||
Addini | Musulunci | ||
Jam'iyar siyasa | National Council for Democracy and Development (en) | ||
IMDb | nm4148457 |
Rayuwar farko
gyara sasheCaptain Camara yayi karatun sa na pramare da na sakandare ne a Nzerekore inda ya samu diploma ta Baccalaureat a fannin lissafi na shiga jami'ya a makarantar lycee Samory Toure. Sannan a 1986 ya shiga Jami'ar Gamal Abdel Nasser dake Conakry, babban birnin ƙasar, inda ya samu digiri a fannin tattalin arziki.
A shekarar 1990, Moussa Dadis Camara ya shiga sojan kasar Guinea inda ya cigaba da samun horon soja a hindia dake da nisan km 137 da birnin Conakry. Bayan shekara shidda wato a shekarar 1996 ya shiga makarantar offissa a Dresde dake nan Jamus, inda ya samu diploma na shugaban sashen Tsimi a Breme kasar ta Jamus, sannan daga nan ya shiga wata rundunar haɗin gwiwa ta sojojin ƙasar Faransa da Jamus. A lokacin da ya dawo daga Turai a shekarar 1999 ya zama ma taimakin mai kula da hukumar soja ta dakarun majalissar dinkin duniya a ƙasar Saliyo. Daga 2000 zuwa 2001 ya riƙe muƙamin shugaban kula da sashen man petur da sojojin ƙasar ta Guinea ke anfani dashi. Ya sake komawa ƙasar Jamus a shekara ta 2004 inda yayi karatun samun muƙamin Captain a makarantar sojojin ƙasa ta Infantry ta birnin Hamburg, kana yaci gaba da ɗaukan darasi kan harkokin da suka shafi sojan sama inda ya samu diploma na sojan leyma Daga 2005 zuwa 2007 Moussa Dadis Camara ya sake riƙe muƙamin shugaban kula da mai da rarrabashi ga soja, na dakarun ƙasar ta Guine sannan a shekara ta 2008 ya zama Darecta Janar na Man Petur, kuma a daidai wannan lokacin yana wani karatun na Babbar cibiyar soja a makarantar sojoji ta EMIAG ta ƙasar Guine.
Yana cikin haka yan sa'o'i kaɗan bayan rasuwar Shugaba Lansana Conte Shugaban ƙasa na biyu a ƙasar ta Guine, sai kawai Capitain Dadis Camara, wanda ma ba'a sanshi haka a bainar jama'a ba, ya fito ta kafofin yaɗa labarai na ƙasar, inda yace ya soke kundin tsarin mulkin ƙasar, da sauran duka manyan ma'aikatu na ƙasa, kamar su majalissar dokoki, Kotun tsarin mulki da dai sauransu, tare kuma da rusar da gomnatin, inda yayi wani jawabi da a cikinsa ya tabo batun halin rishin tabbas da yan kasar suka shiga sakamakon wancan mulki, ya kuma zarge su da wawushe dukiyar ƙasa.
Ranar 23 ga watan disamba na 2008 ne aka naɗa shi a matsayin shugaban majalissar ƙasa mai kula da demokiradiya da cigaban ƙasa CNDD inda washe gari Sojojin ƙasar suka naɗashi a matsayin shugaban ƙasar na mulkin soja. Tun a lokacin nan ne yayi alƙawarin shirya zaɓe na gaskiya a watan disambar na 2010.
Saidai kuma shugaba Dadis Camara ya shiga halin tsaka mai wuya tun lokacin da wasu masu Iza mai kantu ruwa suka fara yi masa huɗubar cewa ya tsaya takara a zaɓen da ya riga yace ba zai tsaya ba, abun da wasa wasa yaci gaba da kawo jayayya a cikin ƙasar ta Guine har ya zuwa ranar 28 ga watan satumba na 2009 inda sojoji suka buɗa wuta a taron gangamin masu adawa da tazarcen nashi abun da ya kawo rasuwar mutane a ƙalla 175. To, a halin da ake ciki dai, ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa - sun buƙaci shugaban dama maƙarrabansa da kada su tsaya takarar, a dai dai lokacin da Majalisar Ɗinkin Duniya, da kuma Kotun hukunta masu laifukan yaƙi suka fara binciken kissar jama'a da kuma fyaɗen da jami'an tsaron ƙasarsuka yiwa mata, a lokacin wani gangamin da 'yan adawar ƙasar suka yi a wani babban filin wasa dake Conakry - babban birnin ƙasar.
A ranar 31 ga Yuli, 2024, an sami Moussa Dadis Camara da laifin "laifi kan bil'adama" a kisan kiyashin da ya faru a 2009, kuma an yanke masa hukuncin daurin shekaru ashirin a gidan yari.