Cordelia Ainenehi Agbebaku (Janairu, 1961 – Fabrairu 16, 2017) Malamar Najeriya ce kuma tsohuwar mataimakiyar shugaban jami'ar Alli Ambrose.

Cordelia Agbebaku
Rayuwa
Haihuwa Ekpoma, 1961
ƙasa Najeriya
Mutuwa Benin, 16 ga Faburairu, 2017
Sana'a
Sana'a mataimakin shugaban jami'a
Imani
Addini Kiristanci

An haifi Agbebaku a Ekpoma a watan Janairu, 1961. Ta yi karatun shari'a a Jami'ar Jihar Bendel a yanzu Ambrose Alli University, Ekpoma.[1] Agbebaku ta zama mataimakiyar shugaban jami’ar Ambrose Alli (AAU) a hukumance a shekarar 2014 lokacin da gwamna Adams Oshiomhole ya tabbatar da naɗin nata.[2] Ta kasance tana aiki a matsayin mai riko tun a shekarar 2011 yayin da take aiki a matsayin shugabar tsangayar doka.[1] Agbebaku ta rasu ne a ranar 16 ga watan Fabrairu, 2017, a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Benin, kuma ta bar ‘ya’ya da mijinta Farfesa Phillip Agbebaku na sashen kimiyyar siyasa a jami’ar.[3]

Duba kuma

gyara sashe
  • Jerin mataimakan shugabannin jami'o'i a Najeriya

Manazarta

gyara sashe
  1. 1.0 1.1 "History of Ambrose Alli University, Ekpoma". Archived from the original on 3 February 2014.
  2. "Appointment of a Substantive Vice-Chancellor For Ambrose Alli University, Ekpoma".
  3. Okere, Alexander. "Ex- AAU VC,Prof. Agbebaku, dies at 55". Punchng.