Chike Olemgbe dan siyasar Najeriya ne a halin yanzu yana rike da mukamin kakakin majalisar dokokin jihar Imo karo na 10 tun watan Yunin 2023. Dan jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Olemgbe yana wakiltar mazabar jihar Ihitte/Uboma a majalisar dokokin jihar. Shi dan majalisa ne na farko. Vitalis Azodo na jam’iyyar APC mai wakiltar mazabar Ideato ta kudu ne ya tsayar da Olemgbe a matsayin shugaban majalisar sannan kuma Ugochukwu Obodo shi ma na jam’iyyar APC mai wakiltar mazabar Owerri Municipal ya tsayar da shi. An zabe shi gaba daya a matsayin shugaban majalisar.

Chike Olemgbe
Rayuwa
ƙasa Najeriya
Karatu
Harsuna Turanci
Harshen, Ibo
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imani
Jam'iyar siyasa All Progressives Congress
Wannan Muƙalar guntuwa ce: tana buƙatar a inganta ta, kuna iya gyara ta.


Manazarta

gyara sashe