Charles Quaker-Dokubo
Charles Quaker Dokubo malami ne ɗan Najeriya kuma tsohon mai baiwa shugaban ƙasa shawara kan Neja Delta kuma kodinetan shirin afuwa na shugaban kasa (PAP).[1][2][3]
Charles Quaker-Dokubo | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | 23 ga Maris, 1952 |
Mutuwa | Abuja, 25 ga Augusta, 2022 |
Karatu | |
Makaranta |
University of Bradford (en) Teesside University (en) |
Sana'a | |
Sana'a | Malami |
Rayuwar farko da ilimi
gyara sasheAn haifi Charles Quaker Dokubo a ranar 23 ga watan Maris, 1952, a Abonnema, ƙaramar hukumar Akuku Toru, jihar Ribas.[4]
Dukkanin karatunsa na firamare da sakandare ya gudana ne a garin Abonnema kafin ya tafi Burtaniya da halartar Kwalejin fasaha ta Huddersfield da ke Yammacin Yorkshire don kammala matakinsa na "A".
Bayan ya sami digirin digirgir a fannin tarihi da siyasa na zamani daga jami'ar Teesside da ke Middlesbrough, Dokubo ya ci gaba da samun digiri na biyu a fannin nazarin zaman lafiya da kuma PhD a kan yaɗuwar makaman nukiliya da sarrafa shi daga jami'ar Bradford a shekara ta 1985.
Sana'a
gyara sasheDokubo Farfesa ne na Bincike a Cibiyar Harkokin Kasa da Kasa ta Najeriya da ke Legas, Najeriya kafin a naɗa shi mai kula da shirin afuwa na shugaban kasa (PAP) a shekarar 2018.[5]
Ya kasance mai kula da rajistar masu kaɗa kuri’a a lokacin zaɓuka na musamman na shekarar 1997 a Laberiya a matsayin memba na kungiyar taimakon fasaha ta kungiyar kasashen yammacin Afirka.[6]
A shekarar 2020 ne shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya amince da dakatar da shi bayan zargin almundahana da dukiyar ƙasa.[7][3]
Manazarta
gyara sashe- ↑ Akekegha, Igho (14 July 2019). "Dokubo: Niger Delta needs to take good advantage of opportunities we are given". The Guardian (Nigeria). Archived from the original on 3 November 2023. Retrieved 4 December 2023.
- ↑ Onukwugha, Anayo (25 August 2022). "Ex-Presidential Amnesty Boss, Dokubo, is Dead". Leadership News.
- ↑ 3.0 3.1 "Why Buhari suspend coordinator of presidential amnesty programme". BBC News Pidgin. 2020-02-29. Retrieved 2022-08-31.
- ↑ Akinwale, Yekeen (March 14, 2018). "New head for amnesty programme as Buhari launches probe into 'financial impropriety'" (in Turanci). International Centre for Investigative Reporting. Retrieved 2022-08-25.
- ↑ "Professor Charles Quaker Dokubo Archives". City People Magazine (in Turanci). Retrieved 2022-08-25.
- ↑ "Charles Quaker-Dokubo". Africa Portal. Retrieved 2022-08-26.
- ↑ Ailemen, Tony (February 29, 2020). "Buhari approves suspension of Charles Dokubo". Business Day. Retrieved 2022-08-25.