Centenary City Nigeria

Birni ne a Abuja, Najeriya
  • centenary
    Cenetary hall
    Birnin Centenary birni ne da aka tsara a Babban Birnin Tarayyar a Najeriya. Centenary City wani babban shiri ne na ci gaba wanda Centenary City FZE ke kula da shi, a wani bangare na hangen nesan Najeriya na samar da birni mai kafin baki a nan gaba tare da layin Dubai, Monaco da Singapore. Za a gina birnin tun daga tushe a kan kadada 1,260 na fili da akayi mai nisan kilomita da yawa kudu maso yammacin babban birnin tarayyar Najeriya Abuja da kilomita biyar daga filin jirgin sama na kasa da kasa.