Caleb Femi
Caleb Femi (an haifeshi a shekara ta 1990) marubuci ne kuma ɗan Najeriya, ɗan ƙasar Burtaniya, mai shirya fina-finai, daukar hoto, haka-zalika tsohon ɗan takarar matasa na Landan. Kundin wakokinsa na farko, mai suna; Poor, an ba shi lambar yabo ta Forward Prize for Poetry.
Caleb Femi | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | jihar Kano, 1990 (33/34 shekaru) |
ƙasa | Najeriya |
Karatu | |
Makaranta | University of London (en) |
Sana'a | |
Sana'a | mai daukar hoto da marubuci |
IMDb | nm9178255 |
Rayuwar farko
gyara sasheAn haifi Femi a shekara ta 1990 a Kano, Nijeriya,[1] inda ya girma a wurin kakarsa.[2] Lokacin da yake ɗan shekara bakwai, ya yi ƙaura domin shiga cikin iyayensa a Arewacin Peckham Estate a Landan.[3] Bayan ya bar makaranta, ya karanci Turanci a Jami'ar, Queen Mary, University of London. [2]
Sana'a
gyara sasheDaga 2014 zuwa 2016 Femi ya koyar da Turanci a makarantar sakandare a Tottenham.[2] A cikin 2016 an zaɓe shi a matsayin wanda ya lashe kyautar matasa na farko a London.[4] A ranar 30 ga Yuli 2020, ya wallafa kundin waƙoƙinsa na farko, mai suna Poor,[5] wanda ya ci Kyautar Forward Prize's Felix Dennis Prize for Best First Collection a cikin watan Oktoban shekarar 2021.[6]
Fina-finai
gyara sasheKawo yanzu Femi ya yi kuma ya fitar da gajerun fina-finai guda huɗu, yana aiki a matsayin marubuci / darakta akan kowanne:[7]
- And They Knew Light (2017)
- Wishbone (2018)
- Secret Life of Gs (2019)
- Survivor's Guilt (2020)
Yabo
gyara sasheAn saka sunan Femi a cikin mujallar Dazed 2021 Dazed100, jerin tsarin sabbin masu tsara al'adun matasa.[8]
Manazarta
gyara sashe- ↑ McConnell, Justine (21 July 2017). "Caleb Femi". writers make worlds (in Turanci). Retrieved 16 November 2020.
- ↑ 2.0 2.1 2.2 Peirson-Hagger, Ellen (28 October 2020). "Caleb Femi: 'Poetry is the art of the people'". New Statesman. Retrieved 14 December 2020.
- ↑ Armitstead, Claire (30 October 2020). "Caleb Femi: 'Henceforth I'm solely preoccupied with being a merchant of joy'". The Guardian (in Turanci). ISSN 0261-3077. Retrieved 16 November 2020.
- ↑ Flood, Alison (3 October 2016). "Poet Caleb Femi named first young people's laureate for London". The Guardian. Retrieved 14 December 2020.
- ↑ "Poor by Caleb Femi". The Poetry Book Society (in Turanci). Retrieved 16 November 2020.
- ↑ Bayley, Sian (25 October 2021). "Kennard, Femi and Sealey win Forward Prizes for Poetry". The Bookseller. Retrieved 25 October 2021.
- ↑ "Caleb Femi". IMDb. Retrieved 20 October 2021.
- ↑ Dazed (6 April 2017). "Vote for Caleb Femi on the #Dazed100". Dazed (in Turanci). Retrieved 20 October 2021.
Hanyoyin haɗi na waje
gyara sashe- Official website Archived 2022-05-26 at the Wayback Machine
- Caleb Femi on IMDb
- Bridget Minamore, "Get Up, Stand Up Now: Q&A with poet and director Charles Femi", Somerset House, 28 August 2019