Byron L. Johnson
Byron Lindberg Johnson an haife shi ga watan Oktoba 12, shekarar 1917 - Janairu 6, 2000, malami ne Ba'amurke ne, masanin tattalin arziki kuma ɗan siyasa wanda ya yi wa'adi ɗaya a Amurka. Wakili daga Colorado daga 1959 zuwa 1961.
Byron L. Johnson | |||||
---|---|---|---|---|---|
| |||||
Rayuwa | |||||
Haihuwa | Chicago, 12 Oktoba 1917 | ||||
ƙasa | Tarayyar Amurka | ||||
Mutuwa | Englewood (en) , 6 ga Janairu, 2000 | ||||
Makwanci | Fairmount Cemetery (en) | ||||
Karatu | |||||
Makaranta | University of Wisconsin–Madison (en) | ||||
Thesis director | Harold Groves (en) | ||||
Harsuna | Turanci | ||||
Sana'a | |||||
Sana'a | ɗan siyasa da Mai tattala arziki | ||||
Wurin aiki | Denver da Washington, D.C. | ||||
Employers |
University of Colorado (en) University of Denver (en) | ||||
Imani | |||||
Jam'iyar siyasa | Democratic Party (en) |
Rayuwar farko da Ilimi
gyara sasheAn haife shi a Chicago, Illinois, duk kakannin Johnson hudu sun kasance Sweden baƙi.[1]Ya kambala karatunsa daga Oconomowoc High School, Oconomowoc, Wisconsin, a shekarar 1933.[2]
Ya sami Digiri a Zane(Arts) a Jami'ar Wisconsin – Madison a cikin 1938, kuma ya kammala Master of Arts (1940) da Ph.D. (1947) a Jami'ar Wisconsin-Madison kuma. Ya auri Catherine (Kay) Teter, na Milwaukee, Wisconsin, a cikin Oktoba, 1938.
Aiki a matsayin masanin tattalin arziki da gina gidaje
gyara sasheJohnson masanin tattalin arziki ne na Hukumar Lafiya ta Jihar Wisconsin daga 1938 zuwa 1942. Ya yi aiki a matsayin ma'aikaci a Ofishin Kasafin Kudi na Amurka daga 1942 zuwa 1944, kuma na Social Security Administration a Washington, D.C. daga 1944 zuwa 1947. Farfesa ne a Jami'ar Denver daga 1947 zuwa 1956.
- ↑ "United States Census, 1930", FamilySearch, retrieved March 9, 2018
- ↑ "Johnson, Byron Lindberg Biographical Information". Biographical Directory of the United States Congress. Archived from the original on June 8, 2007. Retrieved October 11, 2009.