Bubacarr Sanneh (an haife shi a ranar 14 ga watan Nuwambar shekara ta alif 1994) ƙwararren ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne ɗan ƙasar Gambia wanda ke taka leda a matsayin mai tsaron baya ga kulob din Danish Superliga SønderjyskE da kuma ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta kasar Gambia.

Bubacarr Sanneh
Rayuwa
Haihuwa Banjul, 14 Nuwamba, 1994 (29 shekaru)
ƙasa Gambiya
Sana'a
Sana'a ɗan wasan ƙwallon ƙafa
Hanya
Ƙungiyoyi Shekaru Wasanni da ya/ta buga Ƙwallaye
SønderjyskE Fodbold (en) Fassara-
R.S.C. Anderlecht (en) Fassara-
Göztepe S.K. (en) Fassara-
Aarhus Gymnastikforening (en) Fassara-
FC Midtjylland (en) Fassara-
K.V. Oostende (en) Fassara-
Real de Banjul F.C. (en) Fassara-
  Kungiyar kwallon kafa ta Gambia2012-30
AC Horsens (en) Fassara2012-324
 
Muƙami ko ƙwarewa Mai buga tsakiya
Nauyi 75 kg
Tsayi 183 cm

Aikin kulob/ƙungiya

gyara sashe

An haife shi a Serekunda, [1] Sanneh ya fara aikinsa na kwallon kafa tare da Real de Banjul. [2]

A ranar 1 ga watan Satumba shekarar 2014 AC Horsens ta tabbatar, cewa sun rattaba hannu kan Sanneh kan yarjejeniyar lamuni na tsawon lokaci tare da zaɓin siye. Ya fara buga wasansa na farko a ranar 10 ga watan Nuwamba shekarar 2014 da Viborg FF, inda ya buga duka wasan kuma ya zura kwallo a raga. [1] AC Horsens sun yi amfani da zaɓi na siyan, kuma sun sanar da canja wuri a ranar 22 ga watan Afrilu shekarar 2015.[3]

A ranar 5 ga watan Nuwamba shekarar 2017 Sanneh bisa hukuma sanya hannu tare da Midtjylland a kan yarjejeniyar shekaru hudu, tare da canja wuri a lokacin hunturu.[4]

A watan Agustan shekarar 2018, Sanneh ya rattaba hannu kan yarjejeniyar shekaru biyar tare da kulob din Anderlecht na Belgium kan farashin canja wuri da aka yi imanin ya kasance € 8m.[5] Ya buga wasansa na farko na gasa a kungiyar a wasan da suka tashi 1-1 a gida da Royal Antwerp kafin ya ci kwallonsa ta farko a wasan da suka doke Standard Liège da ci 2-1. A watan Agustan shekarar 2019, ya rattaba hannu a kulob din Göztepe na Turkiyya a matsayin aro kafin ya yanke kwangilar ta hanyar amincewar juna. Ya koma Belgium a watan Janairu shekarar 2020 don shiga Oostende a matsayin aro har zuwa karshen kakar wasa.[6] A ranar 25 ga watan Janairu shekarar 2021, an aika Sanneh kan lamunin watanni shida zuwa AGF. An soke kwantiraginsa na Anderlecht a ranar 31 ga watan Agusta shekarar 2021.[7]

A ranar 21 ga watan Fabrairu shekarar 2022, Sanneh ya koma Denmark kuma ya rattaba hannu kan yarjejeniya tare da kulob din Danish Superliga SønderjyskE har zuwa karshen kakar wasa.[8]

Ayyukan kasa

gyara sashe

Ya buga wasansa na farko a duniya a Gambia a 2012. [2]

Kwallayensa na kasa

gyara sashe
Maki da sakamako ne suka jera adadin kwallayen da Gambiya ta ci a farko, ginshikin maki ya nuna maki bayan kowacce kwallon Sanneh.
Jerin kwallayen da Bubacarr Sanneh ya ci
A'a. Kwanan wata Wuri Abokin hamayya Ci Sakamako Gasa
1 Oktoba 9, 2019 El Hadj Hassan Gouled Aptidon Stadium, Djibouti City, Djibouti </img> Djibouti 1-1 1-1 2021 neman cancantar shiga gasar cin kofin Afrika

Kanin Sanneh Muhammed shima kwararren dan wasan kwallon kafa ne. [9]

Girmamawa

gyara sashe

Mutum

  • Gwarzon Dan Wasan Horsen na AC: 2014–15

Manazarta

gyara sashe
  1. 1.0 1.1 Bubacarr Sanneh at Soccerway. Retrieved 18 May 2017. Cite error: Invalid <ref> tag; name "SW" defined multiple times with different content
  2. 2.0 2.1 "Bubacarr Sanneh". National Football Teams. Benjamin Strack-Zimmerman. Retrieved 8 May 2018. Cite error: Invalid <ref> tag; name "NFT" defined multiple times with different content
  3. AC Horsens skriver kontrakt med Bubacarr Sanneh" (in Danish). AC Horsens. 22 April 2015. Archived from the original on 19 August 2016. Retrieved 18 May 2017.
  4. Buba completes Anderlecht move!". www.gambiasports.com. 31 August 2018. Archived from the original on 20 June 2019. Retrieved 31 August 2018.
  5. Fin de prêt pour Bubacarr Sanneh, toujours sous contrat à Anderlecht jusqu'en 2023". SitSportmagazine-FR28 January 2020.
  6. SønderjyskE skriver med Bubacarr Sanneh-SønderjyskE". SønderjyskE (in Danish). 21 February 2022. Archived from the original on 21 February 2022.
  7. FC Midtjylland tester Bubacarr Sannehs lillebror, tipsbladet.dk, 21 November 2017
  8. Bubacarr Sanneh kåret til Årets Fighter|AC Horsens" achorsens.dk
  9. FC Midtjylland tester Bubacarr Sannehs lillebror, tipsbladet.dk, 21 November 2017