Brendan Patrick Donnelly (an haife shi 25 ga Agusta 1950) shahararren ɗan siyasan Burtaniya ne mai goyon bayan Tarayyar Turai kuma tsohon dan Majalisa a Turai.

Brendan Donnelly (dan siyasa)
Member of the European Parliament (en) Fassara

19 ga Yuli, 1994 - 19 ga Yuli, 1999
District: Sussex South and Crawley (en) Fassara
Election: 1994 European Parliament election (en) Fassara
Rayuwa
Cikakken suna Brendan Patrick Donnelly
Haihuwa Landan, 25 ga Augusta, 1950 (74 shekaru)
ƙasa Birtaniya
Harshen uwa Turanci
Karatu
Harsuna Turanci
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa da political adviser (en) Fassara
Wurin aiki Strasbourg da City of Brussels (en) Fassara
Imani
Jam'iyar siyasa Liberal Democrats (en) Fassara
hoton Dan siyasa

An haife shi a Landan, Donnelly ya yi karatu a Kwalejin St Ignatius da ke Tottenham, sannan a cocin Christ Oxford. Ya yi aiki a Ofishin Harkokin Waje daga 1976 har zuwa 1982, lokacin da ya shiga kungiyar Conservative a Majalisar Turai. Daga 1986 zuwa 1987, ya kasance mai bada shawara akan siyasa ga Lord Cockfield, sannan daga 1987 zuwa 1990 ya yi aiki a matsayin mai ba da shawara mai zaman kansa kan Ƙungiyar Tarayyar Turai. Bai yi nasara ba a zaben Majalisar Turai na 1989 a karkashin jam'iyyar Conservative yankin Yammacin London.[1]

Brendan Donnelly

An zabi Donnelly a matsayin memba na Majalisar Turai (MEP) na mazabar Sussex South da Crawley a zaben Majalisar Turai na 1994 na Jam'iyyar Conservative. Daga nan ya bar jam'iyyar, ya ci gaba da zama mai zaman kansa na wani lokaci, sannan ya kafa sannan kuma ya zama mataimakin shugaban jam'iyyar Pro-Euro Conservative Party a zaben 1999 na Turai.[2]

Bai samu nasaran cin zabe ba kuma daga baya ya shiga jam'iyyar Liberal Democrats . Ya tsaya a zaben Turai na 2009 a karkashin lakabin siyasar Yes2Europe.[3] Ya tsaya takara a zaben Turai na 2014 na jam'iyyar 4 Freedom Party (UK EPP). Ya tsaya a zaben Majalisar London na 2021 don Rejoin EU. A kowane hali bai yi nasara ba. Ya tsaya takarar Rejoin EU a watan Yuni 2021 Chesham da Amersham .

Brendan Donnelly

Donnelly darekta ne na Federal Trust kuma, har zuwa 6 ga Maris 2010, ya kasance shugaban Federal Union, a yayin da Richard Laming ya gaje shi.[4]

Manazarta

gyara sashe
  1. BBC-Vacher's Biographical Guide 1996. London: BBC Political Research Unit and Vacher's Publications. 1996. pp. 6–10. ISBN 0951520857.
  2. "BBC News | Parties and Issues | Pro-Euro Conservative Party". news.bbc.co.uk.
  3. "UKPollingReport Election Guide 2010 » London European Elections".
  4. "Chesham and Amersham by-election – Rejoin EU". 14 June 2021.