Bernard Binlin Dadié
Bernard Binlin Dadié (10 Janairu 1916 - 9 Maris shekarar 2019) marubuci ne ɗan Ivory Coast, marubucin wasan kwaikwayo, mawaƙi, kuma mai gudanarwa. Ya kasance Ministan Al'adu a gwamnatin Ivory Coast daga 1977 zuwa 1986. An haife shi a Assinie, Ivory Coast. Ya rubuta labarai na tatsuniyoyi game da mulkin mallaka .[1]
Bernard Binlin Dadié | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Assinie-Mafia (en) , 10 ga Janairu, 1916 |
ƙasa | Ivory Coast |
Mutuwa | Abidjan, 9 ga Maris, 2019 |
Ƴan uwa | |
Mahaifi | Gabriel Dadié |
Karatu | |
Makaranta | École normale supérieure William Ponty (en) |
Harsuna | Faransanci |
Sana'a | |
Sana'a | maiwaƙe, marubuci, ɗan siyasa, marubin wasannin kwaykwayo da marubucin wasannin kwaykwayo |
Muhimman ayyuka | Climbié (en) |
Kyaututtuka |
gani
|
Mamba | Académie des sciences d'outre-mer (en) |
An ga ayyukan Dadié a cikin fim ɗin Steven Spielberg na 1997 Amistad inda aka yi amfani da rubutun baitukan waƙar Dadié, "Ku bushe Hawaye, Afrika" ("Sèche Tes Pleurs") don waƙar suna iri ɗaya.
Ya cika shekaru 100 a cikin Janairun 2016 kuma ya mutu a Abidjan a ranar 9 ga Maris 2019 yana da shekara 103. [2]
Dadié ya sami lambobin yabo da yawa don girmama aikinsa na rubutu, tare da ɗayan na ƙarshe shine Grand Prix des Mécènes na GPLA a cikin 2016.[3]