Benito Owusu Bio
Benito Owusu Bio (an haife shi a watan Nuwamba ɗaya 1, shekarar alif dubu ɗaya da ɗari tara da sittin da takwas 1968)[1][2] masanin tattalin arzikin ƙasa ne[1][2] kuma ɗan siyasar Ghana na Jamhuriyar Ghana. Shi ne dan majalisa mai wakiltar mazabar Atwima-Nwabiagya na yankin Ashanti na kasar Ghana a majalisa ta huɗu 4 da biyar 5 da shida 6 da ta bakwai 7 da kuma ta takwas 8 a jamhuriya ta hudu ta Ghana.[3] Dan sabuwar jam'iyyar kishin kasa ne.[1][2][3]
Rayuwar farko da ilimi
gyara sasheAn haifi Owusu a ranar ɗaya 1 ga watan Nuwamba, shekarar alif dubu ɗaya da ɗari tara da sittin da takwas 1968.[1][2] Ya fito ne daga Akropong, wani gari a yankin Ashanti na Ghana.[1][2] Ya fito ne daga Jami'ar Kimiyya da Fasaha ta Kwame Nkrumah.[1][2] Ya yi digirin farko na Kimiyya a Landan Economy daga jami'a.[1][2] Ya samu digirin ne a shekarar dubu ɗaya da ɗari tara da casa'in da huɗu 1994.[1][2] Ya kuma yi fice a Jami’ar Birmingham.[1][2] Ya yi Masters a fannin zamantakewar al'umma a fannin baƙo.[1][2] Ya samu takardar shedar a shekarar alif dubu ɗaya da ɗari tara da casa'in da takwas 1998.[1][2]
Aiki
gyara sasheOwusu ya kasance babban manaja a Hotel Georgia Limited da ke Kumasi.[1][2]
Aikin siyasa
gyara sasheOwusu memba na New Patriotic Party ne.[1][2][3] Ya zama dan majalisa ne daga watan Janairu, shekara ta alif dubu biyu da biyar 2005 bayan ya zama zakara a zaben gama gari a watan Disamba shekara ta alif dubu biyu da huɗu 2004.[4][5] Tun daga nan ya yi tazarce na wa'adi hudu a jere.[3] Shi ne dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Atwima-Nwabia ta Arewa.[1][2][3][4] An zabe shi a matsayin dan majalisa na wannan mazaba a majalisa ta hudu da ta biyar da ta shida da ta bakwai a jamhuriyar Ghana ta hudu.[3] Ya kasance memba na kwamitin hanyoyi da sufuri da kuma kwamitin kula da harkokin gwamnati a majalisar dokoki ta bakwai 7 ta jamhuriya ta hudu ta Ghana. Yayin da yake majalisar, an nada shi mataimakin ministan filaye da albarkatun kasa.[6]
Zabe
gyara sasheAn zabi Owusu-Bio a matsayin dan majalisa mai wakiltar mazabar Atwima-Nwabiagya ta Arewa na yankin Ashanti na Ghana a karon farko a babban zaben Ghana na shekara ta alif dubu biyu da huɗu 2004.[3][4][5] Ya yi nasara akan tikitin New Patriotic Party.[4][5] Mazabarsa wani bangare ne na kujeru talatin da shida 36 na 'yan majalisa daga cikin kujeru talatin da tara 39 da New Patriotic Party ta lashe a wancan zaben na yankin Ashanti.[7] New Patriotic Party ta samu rinjayen kujeru ɗari da ashirin da takwas 128 na 'yan majalisa daga cikin kujeru ɗari biyu da talatin 230.[8] An zabe shi da kuri'u dubu hamsin da shida da ɗari ukku da talatin da bakwai 56,337 daga cikin dubu saba'in da ɗaru biyu da hamsin da biyu 70,252 masu inganci da aka jefa kwatankwacin kashi tamanin da ɗigo biyu 80.2% na yawan kuri'un da aka kada.[4][5] An zabe shi a kan Ebenezer Obu Tetteh na Peoples’ National Convention, Nana Appia Manu na National Democratic Congress, Munni Issah na Jam'iyyar Convention People's Party da Ben Owusu Boadu na Jam'iyyar Siyasa ta Every Ghanaian Living Everywhere.[4][5] Waɗannan sun sami 1.0% 17.1%, 1.5% da 0.3% bi da bi na jimlar ƙuri'un da aka kada.[4][5]
A shekarar alif dubu biyu da takwas 2008, ya lashe zaben gama gari a kan tikitin New Patriotic Party na wannan mazaba.[9][10] Mazabarsa tana cikin kujeru talatin da huɗu 34 na 'yan majalisa daga cikin kujeru talatin da tara 39 da New Patriotic Party ta lashe a wancan zaben na yankin Ashanti.[11] New Patriotic Party ta lashe kujerun 'yan majalisa ɗari da tara 109 daga cikin kujeru ɗari biyu da talatin 230.[12] An zabe shi da kuri'u dubu arba'in da shida da ɗari shida da biyar 46,605 daga cikin dubu saba'in da biyu da ɗari tara da saba'in uku 72,973 masu inganci da aka jefa kwatankwacin kashi sittin da uku da ɗigo tamanin da bakwai 63.87% na yawan kuri'un da aka kada.[9][10] An zabe shi a kan Chogkureh Christopher na National Democratic Congress da Yaw Frimpong da jam'iyya mai zaman kanta.[9][10] Wadannan sun samu kashi goma sha bakwai da ɗigo bakwai 17.07% da goma sha tara da ɗigo shida 19.06% na jimillar kuri'un da aka kada.[9][10]
A shekarar alif dubu biyu da goma sha biyu 2012, ya lashe zaben gama gari a kan tikitin New Patriotic Party na wannan mazaba.[13][14] An zabe shi da kuri'u dubu ashirin da bakwai da ɗari huɗu da hamsin da shida 27,456 daga cikin duhu arba'in da biyar da ɗari takwas da arba'in da tara 45,849 masu inganci da aka jefa kwatankwacin kashi hamsin da tara da ɗigo tamanin da takwas 59.88% na yawan kuri'un da aka kada.[13][14] An zabe shi a kan Anthony Bernard Ansah na National Democratic Congress, Kwadwo Amponsah na jam'iyyar Progressive People's Party da Dickson Osei-Asibey dan takara mai zaman kansa.[13][14] Wadannan sun samu kashi goma sha takwas da ɗigo biyu 18.2%, sifili da ɗigo tamanin da huɗu 0.84% da ashirin da ɗaya da ɗigo takwas 21.08% bi da bi na jimillar kuri'un da aka kada.[13][14] An sake zaben Benito a zaben shekara ta alif dubu biyu da sha shida 2016 da 2020 don wakilci a majalisar dokoki ta bakwai 7 da ta 8 takwas na jamhuriya ta hudu 4.
Rayuwa ta sirri
gyara sasheOwusu-Bio Kirista ne kuma memba na cocin Anglican.[1][2] Ya yi aure tare da yara uku.[1][2]
Manazarta
gyara sashe- ↑ 1.00 1.01 1.02 1.03 1.04 1.05 1.06 1.07 1.08 1.09 1.10 1.11 1.12 1.13 1.14 1.15 "Ghana MPs - MP Details - Owusu, Benito Bio". 2016-05-06. Archived from the original on 2016-05-06. Retrieved 2020-08-02.
- ↑ 2.00 2.01 2.02 2.03 2.04 2.05 2.06 2.07 2.08 2.09 2.10 2.11 2.12 2.13 2.14 2.15 "Ghana MPs - MP Details - Owusu, Benito Bio". 2016-04-24. Archived from the original on 2016-04-24. Retrieved 2020-08-02.
- ↑ 3.0 3.1 3.2 3.3 3.4 3.5 3.6 "Parliament of Ghana". www.parliament.gh. Retrieved 2020-08-02.
- ↑ 4.0 4.1 4.2 4.3 4.4 4.5 4.6 FM, Peace. "Ghana Election 2004 Results - Atwima Nwabiagya South Constituency". Ghana Elections - Peace FM. Retrieved 2020-08-02.
- ↑ 5.0 5.1 5.2 5.3 5.4 5.5 Elections 2004; Ghana's Parliamentary and Presidential Elections. Accra: Electoral Commission of Ghana; Friedrich Ebert Stiftung. 2005. p. 121.
- ↑ https://mlnr.gov.gh/index.php/deputy-minister-forestry/
- ↑ "Statistics of Presidential and Parliamentary Election Results". Fact Check Ghana (in Turanci). 2016-08-10. Retrieved 2020-08-02.
- ↑ FM, Peace. "Ghana Election 2004 Results - President". Ghana Elections - Peace FM. Retrieved 2020-08-02.
- ↑ 9.0 9.1 9.2 9.3 FM, Peace. "Ghana Election 2008 Results - Atwima Nwabiagya South Constituency". Ghana Elections - Peace FM. Retrieved 2020-08-02.
- ↑ 10.0 10.1 10.2 10.3 Ghana Elections 2008. Ghana: Friedrich Ebert Stiftung. 2010. p. 59.
- ↑ FM, Peace. "Ghana Election 2008 Results - Ashanti Region". Ghana Elections - Peace FM. Retrieved 2020-08-02.
- ↑ FM, Peace. "Ghana Election 2008". Ghana Elections - Peace FM. Retrieved 2020-08-02.
- ↑ 13.0 13.1 13.2 13.3 FM, Peace. "Ghana Election 2012 Results - Atwima Nwabiagya North Constituency". Ghana Elections - Peace FM. Retrieved 2020-08-02.
- ↑ 14.0 14.1 14.2 14.3 Elections 2012. Ghana: Friedrich Ebert Stiftung. p. 148.