Battle of Kwatarkwashi
Yaƙin Kwatarkwashi wani gagarumin yaƙi ne tsakanin Turawan mulkin mallaka na Arewacin Najeriya da kuma sojojin masarautar Kano ta Khalifancin Sakkwato . Kashin da sojojin dawakan kano suka yi a yanƙin ya nuna yadda masarautar Kano ta kaure .
Iri | faɗa |
---|---|
Kwanan watan | 27 ga Faburairu, 1903 |
Wuri | Jihar Zamfara |
Participant (en) |
Fage
gyara sasheA cikin shekarar 1899, Lord Lugard ya shelanta mulkin mallaka na Birtaniyya a kan yawancin Daular Sokoto. Tare da gazawar diflomasiyya da yawa ga Halifa, a cikin shekarar 1900 aka ƙaddamar da yaƙin soja don murkushe halifanci. a lokacin da labarin yaƙin Kano da fadowar kagara ya iso Sokoto a watan Fabrairun shekarar 1903, sai sojojin dawakan Kano suka yi tattaki domin ƙwato garin.[1]
Yaƙi
gyara sasheBayan arangama guda uku da suka yi da sojojin Birtaniya a baya, wani katon Sojan Birtaniya daga Kano ya yi wa sojojin Kano kwanton ɓauna a manyan duwatsun Kwatarkwashi. Bayan an shafe sa'o'i 6 ne aka yi arangama, rasuwar Wazirin Kano ya sa sauran sojojin dawaki suka koma Sokoto, wani ɓangare mai tsoka na rundunar amma a ƙarƙashin Muhammad Abbas ya miƙa wuya ga turawan Ingila ya koma Kano.[2]
A Kano aka kuma naɗa Muhammad Abbas Sarkin Kano. Dakarun dawakan Kano na ƙarshe sun haɗe cikin rundunar Halifa ta Sakkwato.
Duba kuma
gyara sasheManazarta
gyara sashe- ↑ "Fall of Kano". West Gippsland Gazette. 19 May 1903. p. 6 – via National Library of Australia.
- ↑ Ikime, Obaro (1977). Fall of Nigeria. Heinemann. ISBN 0435941402.