Providus Bank PLC ( PB ), banki ne mai ba da sabis na kudi ne na Najeriya, mai lasisi a matsayin bankin kasuwanci, daga Babban Bankin Najeriya da kuma masu kula da harkokin banki na kasa. [1][2]

Bankin Providus Ltd
Bayanai
Suna a hukumance
Providus Bank Limited
Iri commercial bank (en) Fassara da financial institution (en) Fassara
Ƙasa Najeriya
Aiki
Ma'aikata 400
Kayayyaki
Mulki
Hedkwata Victoria Island, Lagos
Tarihi
Ƙirƙira 2016

providusbank.com

Hedkwatar da babban reshe na wannan banki suna a 724 Adetokunbo Ademola Street, Victoria Island, Lagos, a cikin birnin Lagos, babban birnin kasuwanci na Najeriya.[3] Lambobin wuri na hedkwatar bankin sune: 6°25'53.0"N, 3°25'50.0"E (Latitude:6.431389; Longitude:3.430556).[4]

Tun daga watan Nuwambar 2018, Bankin Providus ya yi rajista a matsayin bankin kasuwanci na yanki, yana hidima ga abokan ciniki a jihar Legas da kuma a cikin Babban Birnin Tarayyar Najeriya.[5] Bankin yana da burin yi wa manyan kamfanoni hidima, hukumomin gwamnati, cibiyoyi, ƙanana da matsakaitan masana’antu da kuma manyan mutane attajirai.[6]

Babban bankin Najeriya ya ba bankin lasisin gabatar da hidimar banki na yanki acikin watan Yunin 2016.[7]

Duba kuma

gyara sashe

Manazarta

gyara sashe
  1. "Obinna, Chima (15 June 2016). "CBN Grants Providus Bank Commercial Banking Licence". This Day. Lagos. Retrieved 5 November 2018.
  2. Empty citation (help)
  3. Obinna, Chima (15 June 2016). "CBN Grants Providus Bank Commercial Banking Licence". This Day. Lagos. Retrieved 5 November 2018.
  4. Central Bank of Nigeria (5 November 2018). "Central Bank of Nigeria: List of Supervised Commercial Banks". Abuja: Central Bank of Nigeria. Retrieved 5 November 2018.
  5. Omidire, Dolapo (29 April 2017). "Updated–Development: Providus Commercial Bank Headquarters, Victoria Island–Lagos". Lagos: Estateintel.com. Retrieved 5 November 2018.
  6. Google (5 November 2018). "Location of the headquarters of Providus Bank Limited" (Map). Google Maps. Google. Retrieved 5 November 2018.
  7. City People (1 July 2019). "Meet The Big Boys And Ladies Who Run Providus Bank". City People Online. Lagos. Retrieved 2 February 2020.

Hanyoyin haɗi na waje

gyara sashe