Azubuike Godson Okechukwu (An haife shi ranar 19 ga watan Afrilu, 1997). ɗan wasan ƙwallon ƙafa ta ƙasar Najeriya da ke buga ƙwallo a ƙungiyar clubstanbul Başakşehir ta kasar Turkiyya a matsayin ɗan wasan tsakiya.

Azubuike Okechukwu
Rayuwa
Haihuwa Katsina, 19 ga Afirilu, 1997 (27 shekaru)
ƙasa Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan wasan ƙwallon ƙafa
Hanya
Ƙungiyoyi Shekaru Wasanni da ya/ta buga Ƙwallaye
Yeni Malatyaspor (en) Fassara-
Bayelsa United F.C.2012-2015
Yeni Malatyaspor (en) Fassara2015-
 
Muƙami ko ƙwarewa Mai buga tsakiya
Lamban wasa 14
Nauyi 68 kg
Tsayi 170 cm
Azubuike Godson Okechukwu a yayin fafatawa

Tashe gyara sashe

An haifeshi a Katsina, Okechukwu ya bugawa ƙungiyoyin Bayelsa United da Yeni Malatyaspor ƙwallon ƙafa.

A ranar 19 ga watan Agusta 2018, Okechukwu ya koma ƙungiyar Pyramids FC ta Premier ta Masar.[1][2]

A watan Janairun 2019, ya koma Çaykur Rizespor a matsayin aro har zuwa karshen kakar wasa ta bana. A ranar 10 ga Yulin 2019, İstanbul Başakşehir ya tabbatar, cewa sun sanya hannu kan Okechukwu kan yarjejeniyar aro na tsawon lokaci. [3] Ya lashe gasar ta Turkiyya tare da kulab din.

A watan Agusta na 2020, Okechukwu ya sanya hannu kan kwangilar dindindin tare da İstanbul Başakşehir.

Ƙungiyoyin Duniya gyara sashe

Okechukwu ya fara buga wa ƙasar wasa ne a ƙungiyar kwallon kafa ta kasa a shekarar 2016, kuma Najeriya ce ta zabe shi a cikin jerin 'yan wasa 35 na wucin gadi da za su buga gasar Olympics ta bazara ta 2016.

Manazarta gyara sashe